Responsive Ads Here

Sunday, February 17, 2019

Wasu 'yan Fadakarwa.



HAWAN JINI (HYPERTENSION):

CIWON ZUCIYA (HEART FAILURE):

Menene banbancin wadannan cutuka biyu kuma duka za a iya daukan su daga wani zuwa wani?

Hawan jini: kamar yanda kowa ya sani shine hauhawan bugawar zuciyar daga matakin kididdigar bugun ta zuwa sama bayan la'akari da shekarun kowane mutum. Bugawar zuciyar dan Adam nada alaka da shekarun sa. Dan haka da zaran bugun ya karu ta hanyar aikin ta na Samar da jini da kuma rarrabashi ajiki sai a tabbatar da jijin mutum ya hau.

Shin za'a iya daukan wannan ciwo daga mai shi?

A a wani ba zai iya lakaba ma wani hawan jini ba idan aka debe wata hanya ta gado daga uwaye da kakanni. Kenan auren mutum mai hauwan jini, ko zama damai hawan jini, ko tarayya dashi ko mu'amula duka bazasu sa akamu da cutar hawan jini ba.

Ciwon zuciya  Ko Heart failure shin ko yana nufin karancin aikin zuciya gaba daya?

Shima haka Ciwon Zuciya ba a daukan sa daga wani zuwa wani sannan bazaisa aki tarayya da mai Shiba, ziwon zuciya bayasa aki auren mai shi sannan matsala ce wacce tai hannun Riga da hawan jini.

Kamar yanda kowa yasani kowace cuta tana bukatan kulawa sannan ana bukatan daukan mataki da wuri daga lokacin da aka fahimci akwai cutar ko akaga wasu alamomi nata. Haka ma ga wadannan cutuka biyu mabanbanta.

Dan haka wajibi ne da zaran kaji wata alama wacce bakasanta ba kaje asibiti mafi kusa dan daukan mataki da wuri.
Allah yasa mu dace ameen.




KO KA SAN CHOLESTEROL?


Wani irin sinadari ne da jikin dan adam ke amfani dashi domin gudanar da wasu ayyukan lafiya a cikin jinin mutum.

Wasu daga cikin ayyukan cholesterol a cikin jini sune: 

1. Sauye-sauyen halittar dan adam yayin da yake balaga da kuma sarrafa sha'awar sa.

2. Dai-daita sukari a cikin jini

3. Kare mutum daga daukar wasu cututtuka ( kamar su infection, Fungals da kuma Virus).

4. Samarda Vitamin Rukunin D (sinadari maisa kwarin Qashi da kuma kwarin hakora) da sauransu.

Cholesterol dai sinadari ne mai danko kamar kitse. Idan yayi yawa a cikin jini yana likewa a hanyoyin jini dake daukar jini (artery) zuwa zuciyar dan adam. 

Faruwar haka na iya haddasa toshewar fayif din hanyoyin jinin (wato plague/atherosclerosis a turance), da hakan ta faru sai Hanyoyin dake kawo jini zuwa zuciya su toshe (Coronary artery disease). Daga nan sai a samu "heart attack" (zuciyar mutum ta samu Matsala ko mutum ya mutu).

Ko kuma Zuciya ta kasa harba jini zuwa sauran hanyoyin jini na sauran jikin mutum (heart failure).

Sauran abinda Cholesterol yake haddsawa sun hada da:

1. Hawan Jini.

2. Ciwon suga.

3. Paralyse, (Mutuwar Bangaren jiki).

5. Obesity, (Nauyi ya mai wuce Kaida).

6. Free Mature ejaculation (Raunin Al'aurar Namiji Yayin Saduwa).


Abubuwan da ke saka wannan Cholestoral din Ya ya waita a jikin Mutum kuwa Sune;

1. Yawan cin lipo Protein.
 kamar su:- Nama, Kwai.

2. Kayan Gwangwani, (Can food), misali Kifin Gwangwani, lemon Gwangwani , naman Gwangwani, dasauransu.

3. Yawan cin Saturated fatty acid, kamar Su; Butter, chocolate ,yawan shan Madara.

4. Yawan cin Kayan (Poultry) kamar Kajin Gidan gona, kifin Gidan gona, da sauransu.

5. Cin kitse ( Fat) Babbar musiba ce dake Sabbaba Samuwar cholesterol a jikin Dan Adam.

6. kwanciya nan Take bayan Cin abinci, kafin Narkewar sa da 2hours Awa Biyu.


Maganin dai-dai tuwar wannan Sinadiri na Cholesterol:

1- Motsa jiki. Babbar Hanya ce ta yakar yawan Cholesterol .

2- Cin Ganye da yawa.

3- Shan Ruwan Dumi,
shi kadai, bayan an gama cin Abinci.

4- Saka Lemon Tsami a cikin abinci ko abin sha.

5- Amfani da waken Soya Beans.

6- A Samu Tafarnuwa kwaya 10, da lemon Tsami guda 5, da Ruwa madaidaici kamar Babbar Robar Swan ko Faro, a markade Su a Blanda a Hade, a rinka Shan Ruwan bayan cin Abincin Rana ko na Dare a kullum har Zuwa kwana 10.


7- Nisantar dukkan Kayan Maiko, ko daina Cin Kitsi baki daya.

Yana da kyau Duk Wanda Yaga Wannan Sako Yayi kokari Ya turawa ko yasanarda  Wasu domin Bamu San wayake cikin wannan Matsalar ba Ya kasa samun Mafita.




A gaisheku Yaran Shago, domin a tafiyar tamu babu waige!


.....Ina miqa saqon gaisuwa zuwa ga Uncle Farooq (shugaban 'yan No Free), tareda fatan Mal. Abdul MD (Amudah) zaka isarmin da wannan saqon nawa wajen malami Na.




via: Dom-Domty Medical Tips.
Mustapha Abdulmumin
the2brothers.


0 comments:

Post a Comment