Responsive Ads Here

Friday, February 1, 2019

Ciwon Kai Bari daya (Migraine)

CIWON KAI NA "MIGRAINE"



Ciwon Kai Na ‘Migraine’: Yana daga cikin cutukan da mata sukafi addaba, Sai de wasu lokutan yana addabar wasu maza kalilan, amma dai mata ne suka fi fama dashi.

Ciwon kai ne mai tsanani mai zuwa kusan wata-wata kamar al’ada. Ya fi kama 6ari daya na kan, kuma mace za ta rika jin alamu kafin yazo, wadanda ke nuni da cewa ciwon ya kusa zuwa.

Wadannan alamu sun hada da:
Rashin son haske ko kara, ganin walkiya-walkiya da sauransu. A wasu lokutan kuma ba alamun, sai dai kawai ciwon kan ya sauko.

Sauran alamun ciwon sun hada da yawan tashin zuciya, ko amai.

Matsalar bata cika tafiya da magungunan kashe zogi na Panadol ko Ibuprofen ba. Dole sai anba mutum magunguna masu karfi, matsalar take lafawa.
Don haka idan mutum na fama da irin wannan matsanancin ciwon kai, dole sai yaje wurin likita ya rubuta mata magani mai karfi.

Shi dai ciwon har yanzu ba a tantance me yake kawo shi ba, amma an dai san yana bin zuri’a, wato uwa takan sawa ’yarta. Wato kenan yana da alaka da gado.

Sauran abubuwan da aka danganta da matsalar sune shan kwayoyin tazarar haihuwa wato pills da samun juna biyu da tsayawar al’ada a mata idan sun manyanta.

Akwai ire-iren abinci da abunsha da kan tayar da ciwon irinsu barasa ds, wadanda su masu matsalar ya kamata su lura su guje musu. Sai kuma rashin samun isasshen hutu, da kuma Aje wayoyin salula, laptop da sauran electronic gajet kusa da gadajen mu yayin bacci, ha ka yawan zama kallon film shima an tabbatar yana saurin sa tashin ciwon.

0 comments:

Post a Comment