Responsive Ads Here

Wednesday, February 13, 2019

Ruwan Kwakwa

Ko Kun San? 


Amfanin Ruwan Kwakwa Da Madarar Kwakwa A Jikin Dan’adam:

Kwakwa wacce a Turance muka sani da Coconut ta kasance daya daga cikin muhimman tsirran itatuwa masu zama a matsayin abinci da kuma magani na musamman.

Lokuta da dama za ka ga mutum ya shagaltu da cin wani abu na daban da cinsa baya da wani amfani ga jiki kuma ya kasa daina cin wannan abin.Haka kuma za ka tarar mutum na cin wani abu da baima san amfanin cinsa ba amma kuma sai a tarar yana amfanar jikinsa.


Ganin haka yasa muka dukufa da zakulo tsirran itatuwan da Allah ya albarkacemu dasu anan kasar. Tsirran itatuwan dake zama a matsayin abincin dake gina jiki, inganta lafiya da kuma maganin cututtuka.

A kan samu ruwan kwakwa a lokacinda aka fasa kwakwa sai a rabata biyu to za a ga wadannan ruwan dake kumshe da irin wasu sinadirai kama daga na Bitamin B1,B2,B3,B5,B6,B7,B9, Calcium, potassium, vitamin C da sauransu.


Fa'idodin Ruwan Kwakwa:

✓- Daya daga cikin manyan fai’dodin ruwan kwakwa shi ne saurin maido da karfin jiki a bayan da aka sha wahala na yanayin wani aiki ko jinya ta rashin lafiya.
Sai a nemi lita daya ta ruwan kwakwa a rinka kwankwada za a ji garau a jiki.

✓- Ruwan kwakwa na kara yawan ruwan jiki.

✓- Ruwan kwakwa na baiwa jiki kwari da karfi na jiyoji da kassa.

✓- Ruwan kwakwa na tafiyar da gajiya da ciwon jiki bayan fama da wani aiki na wahala ko doguwar tafiya.

✓- Ruwan kwakwa na maganin ciwon suga amma akwai bukatar nazari da bayani a yayin wannan hadin.

✓- Ruwan kwakwa na kare koda daga barazanar ciwon koda.

✓- Ruwan kwakwa na rage hauhawan jini.

✓- Suna gyara lafiyar ciki su warkar da wasu cutuka kamar na kumburin ciki da tashin zuciya ko yawan gyashi.

Karfin fahimta da aikin kwakwalwa sai a nemi dabino da zuma da ruwan kwakwa.


Madarar Kwakwa:

Wannan madarace amma kuma ba irin wacce muka sani ba.
Madara ce da sai an nika kwakwar sannan ake samunta.

Wannan ne ya sa madarar Peak har yanzu ita ce a kan gaba saboda ana hada madarar ne da kwakwa.

Rabin kofi daya na Madarar kwakwa na kumshe da calories 138, Gram daya da rabi na protein, gram 2 na sugar da kuma grams 14 na fat. Sai 5.5 milligrams na manganese, milligrams 15 na copper, 60 na phosphurus, 22 na magnesium, sai 3.9 na Iron da kuma 4.5 na potassium. Kashi hamsin na maikon dake a cikin madarar kwakwa lauric acid ne wadanda ke magance kwoyoyin cuta.

✓- Madarar kwakwa na gina jiki ta bada karfi wa jiki ta kuma zamo sojojin da za su kare jiki daga farmakin wasu cututtuka.

✓- Mai fama da ciwon gabobin jiki zai iya fake amfani da madarar kwakwa tana magani sosai.

Na so in yi ta kawo fa’idodin amma zan takaita anan tare da fatar za a amfana.



Ko kasan amfani na hadin madara da zuma?

Hadin madara da zuma wani hadi ne na musamman dake da matukar tasiri da alfanon gaske ga lafiyar jikin dan’Adam.

Kasancewa da dama muna amfani da zuma haka kuma muna shan madara a yau da kullum sai dai kuma bamu cika hada madara da zuma a waje daya ba. Gabaki daya wasu ba su taba yin wannan hadin ba, wanda wannan bai rasa nasaba da rashin sanin alfanon yin hakan ba.

A dalilin haka ya sa na zo da wannan bayanin da manufar fadakarwa da kuma ilmantarwa kan alfanon shan hadin madara da kuma zuma a waje daya.

Allah ya sanya zuma ta kasance wata kariya da kuma magani ga dimbin cututtukan dake damun dan’Adam.


✓- Zuma tana dauke da wasu sinadirrai masu karfafa garkuwar jiki dan samun damar yakar kwayoyin cuta a jiki.

✓- Tana maganin cututtukan da suka kama wasu muhimman gabobin jiki da gangar jiki gami da jini da fata.

✓- Zuma na kumshe da sinadiran:
calcium, copper, Iron, magnesium, manganese, ph acid, da flabonoids, riboflabin, pantothenic acid, niacin, thiamine da makamantansu.

A yayin da madara take a cikin tsarin abinsha nau’in protein mai daukeda sinadiran kamar su :
Bitamin A, Bitamin B1, Bitamin B2, Bitamin B3, Bitamin B6, Bitamin B12,Bitamin C, Biotin,Bitamin D, Bitamin E, Folate, Pantothenate, Calcium, Choloride, Copper ,Iron, Iodine, magnesium, Manganese, Selenium, sodium da kuma zinc.

Anan da wadannan sinadiran dake a cikin zuma da kuma wadanda ke a cikin madara, hada zuma da madara tamkar ninka wadannan sinadirran ne a waje daya.

Madara Ta Kasu Gida Biyu, Hakama Zuma Ta Kasu Gida Biyu:



1- Akwai madarar da aka sarrafa, wannan madarar tana zuwa a cikin leda ko gwangwani kamar irin peak milk za a iya amfani da ita a hada da zuma. Wasu sun fi bukatar amfani da ita domin an tsabtaceta daga dukkanin wani abu da zai iya cutarwa.


2- Sai kuma madara da ba a sarrafa ba waton wacce ake tatsowa kai tsaye daga Saniya. Wannan na kumshe da sinadiranta da ba a rage ko aka kara komai daga gare ta ba.

Sai dai kuma a kan samu gaurayewar kwayoyin cuta a yayin da ake tatso madarar ko daga abin da aka yi amfani da ita a tarar tana da datti ko saniyar ba ta da lafiya.
Haka kuma ana iya tafasa madara sai dai kuma idan aka tafasata to akwai wasu sinadiran da zafin wuta ke kasha wa.

Zuma ta kasu gida biyu:
1- Akwai wacce aka sarrafa kamar wacce muke gani a cikin gongoni ko kwolbar da aka sayo daga wani kamfan.
2- Akwai wacce Kai zaye aka daukota, ma'ana wata company bata sarrafata zuwa cikin kwalba ko gon-goniba.
Wannan zumar ba ta da karfi kamar wacce ba a sarrafa ba. Dan haka idan za ka iya sawo zumar da aka debo kai tsaye to tafi yin magani fiye da wacce aka tace aka sanya a kwolba ko gwangwoni.
Haka kuma a kiyayi tafasa zuma domin zafin wuta na kashe sinadarin dake a cikinta.


Hadin zuma da madara yana da alfanu sosai kamar haka :

✓- Yana maganin cututtukan ciki, rugugin ciki, zafin ciki, ciwon ciki, kumburin ciki tashin zuciya da kuma tsiwar hanji.

✓- Hadin zuma da madara na maganin yawan gajiya, kasala, rashin kuzarin jiki,ciwon da kuma gabobin jiki.

✓- Hadin zuma da madara na karfafa kwarin jiki, karfin jiki, karfin jiyoji, karfin da kuma hakora.Saboda samuwar sinadiran calcium a cikin madara da kuma zuma.

✓- Yana samar da hutu da samun isashen bacci ga jiki bayan tsananin kasala ko gajiya a dalili da tafiya ko aiki.

✓- Magani ne ga dimbin cututtuka da kuma fungi ke haddasawa. Sai a rinka hadin zuma da tafarnuwa a sha.

✓- Tari da sanyi na mura. Sai a nemi tafarnuwa a yanka kamar yankan albasa a hada da zuma cokali uku da safe sai a sha.

✓- Idan kana fama da gyambon ciki, sai a rinka shan wannan hadin.

✓- Karfin gani da inganta karfin kwakwalwa.

✓- Yana rage barazanar kamuwa da hawan jini.

✓- Yana gyara lafiyar fata,kyalkyalin fata,fata mai laushi.


Kuna iya yimana comment a kasa, domin fadin ra'ayoyinku ko Kuma bayarda shawar-wari! 





════════════════════

مصطفى عبدالمؤمن-
the2brothers


2 comments: