Responsive Ads Here

Friday, January 18, 2019

Domin Yaranmu

DIYAWA DAGA CIKIN MATA SUNA SO SUGA YARANSU SUNA DA JIKI , WASSU ZA KASAMESU SUNA DURAWA YARO MULTIVITAMINS KAWAI SABIDA SUGA YARO YAYI KIBA .


TO GA HANYA :

1- Exclusive Breast feeding up to 6months .

Shayar da yaro nono zallah har zuwa watanni shidda , ba tareda anbada ko ruwa ba .

Kuma a tabbata duk sanda za abawa yaro nono yazama bakin nonon yashiga bakin yaro sosai idan baishiga sosai yaro bazai samu ruwan nono yadda yakamata ba.

Kuma Idan ansa yaro a nono , bari yasha sai yagaji da kansa yabari , kuma kada a ace za'a canza masa nono lokocin da yana shan nono .

2- IMMUNIZATION

Immunization wata hanyace tabawa yara kanana kariya daga kamuwa da cututtuka wanda zai maida yaro baya wajen girma  ko kiba ga kadan daga cikin cututtukan :

- Tarin TB
- Cutan hanta
- Shan inna
- Tarin kototo
- Tsarka hakora
- Tarin nimoniya
- Tarin influenza
- kyenda
- shawara
- cholera .

3- Nutrient .

Idan yaro ya cika watanni shidda abincin da za abashi yakamata yazama nutrient .

Menene nutrient shine abincin da yake dauke da components of food kamar proteins, carbohydrate , fat , minerals , vitamin da sauran su .

Wani zai iya tambaya tayaya zan hada wadannan sinadaran abincin lokoci guda ? To ga hanyar sauki :

1- Kisamu Gyero ko masara ko shinkafa ko alkama alal misali Kopi shidda (6). an samu carbohydrate .

2- Kisamu Wake , ko waken suya Kopi uku (3) ansamu protein.

3- Asamu Gyeda Kopi 1 ko 1.5 (Kopi daya ko daya da rabi ) ansamu fat and oil .

Adan soyasu kadan dan sabida suyi kamshi ahadasu waje daya a nuka yazama garin kunun yaro , anadamawa ana saka sugari a dinga bawa yaro insha Allah za aga yaro yana girma yadda yakamata .

Kuma adinga bawa yara kayan itatuwa kamar su lemu , ayaba , da sauransu .

Kuma kada asaya a kunu adinga gwada musu abinci , sabida su koyi yadda akecin abinci .

KUSKURE NA KARSHE KUMA ::

Duk sanda za a yaye yaro daga nono dan Allah kada a yaye yaro lokoci guda a musu hikima .

Ga hikiman yadda yake :

Idan kina bawa yaronki nono saw biyar a rana sai kimayar saw 4 a rana yauda gobe za amayar so uku , haka yauda gobe sai amayar saw 2, 1 idan akai haka duk sanda aka yaye bazai damu ba .

Bayan wannan wassu matan idan sun yaye yaro sai sudauki yaro sukai gidan kakanta sabida wai ya manta da nonon.

Daganan yaro zai shiga stress , kullum kuka yanaso yaga mamarta , ba cin abinci sai aga yaro yana ramewa sosai , bayan kwana kadan yaro ba lafiya , babu abinci immunity duk sunyi weak , ana zuwa asibity sai ace Malnutrition.


via; Dom-Domty Medical Tips.

0 comments:

Post a Comment