Responsive Ads Here

Thursday, January 3, 2019

GYENBON CIKI

*GYENBON CIKI*


via; Dom-Domty Medicine Store🏥 Gombe.

*Gyenbon ciki* shine idan ansamu kurji ya girma a cikin mutum , da kuma babban hanji haka kuma yakan iya girma a makogoro .

1- Gastric Ulcer : wannan Gastric ulcer wassu suna Kiranta da stomach Ulcer ( ma'ana kurjin ciki ) wannan kurjin yakan kama cikin mutun ne inda abinci yake taruwa .

2- Duedenal Ulcer : wannan shima kurji ne a cikin dan Adam amma wannan kurjin ana samun shi a  Karamin Hanjin Dan Adam.

3- Esophage Ulcer : itama wannan kurjin cikin ne wanda yake girma a makogoro .

*Me Yake kawo gyenbon ciki* :

1- mafi yawan gyenbon ciki kwayar cutar bakteria mai suna HPylori yake kawo shi .

2- sai kuma yawan shan maganin dauke  ciwo kamar su  Ibuprofen , cataflam , Aspirin , naproxen da sauran su .

Baya ga yawan shan maganin dauke ciwo akoi wassu abubuwa da suke taimaka kamar su :

1- Abinci mai dauke da yawan acid

2- Shan taba yakan kara hatsarin kamuwa da gyenbon ciki .

3- shan barasa shima yakan kara hasarin kamuwa da gyenbon ciki sabida yana dauke da acid

4- Sai kuma yawan damuwa bazai haddasa gyenbon ciki ba amma yakan sa ciwon ulcer yayi tsanani ga wanda dama yake da gyenbon cikin.


Gyenbon ciki yana zuwa da alamu da dama, daga cikinsu akoi :

1- Ciwon kirji
2- Ciwon ciki
3- amai ko aman jini
4- kashi da jini
5- ciwon tsakiyar baya
6- Kumburin ciki
7- jin damuwa bayan cin abinci
8- Ramewa mara dalili
9- Tashin zuciya
10-  rashin cin abinci da hajijiya .

*Yaya za'a warkar da gyenbon ciki ??*

Hanyar warkar da gyenbon ciki ta farko shine kawar da da kwayar cutar H- Pylori .

Kuma rage acid da ciki yake fitarwa da hanyar amfani da magunguna masu rage fitar da acids zai taimaka wajen warkarwa .

Kuma yana da amfani mutum yadaina wadannan abubuwa :

- Shan taba
- shan barasa
- Abinci mai dauke da acid
- Abinci mai daci
- abinci mai yaji
- abinci mai dauke da gas kamar coke .

Warkar da kwayar cutar bakteriya mai suna H-pylori yana bukatar a hada maganin rage ko kashe kwayar cutar baktriya a kalla kala biyu . kuma za'a ayi amfani da magunguna masu rage fitar acid a ciki .

Kafin a kawar da kwayar cutar mai suna H Pylori zai dauki lokoci mutum yana amfani da magani a kalla sati biyu zuwa uku . kuma maganin rage fitar acid akalla mutum zaisha zuwa watanni shidda , mafi yawan gyenbon ciki yana warkewa a tsakanin wannan lokocin .

Bayan mutum yayi amfani da magani idan alamar gyenbon cikin suka sake zuwa zaka iya bada wani maganin daban ko kuma kabada shawara mara lafiya yadinga shan maganin ko yadaina jin alamar gyenbon cikin , amma a rage girman ( mg) na maganin .

Daga; *Shagon Magani Na Dom-Domty*🏥dake Gombe.

0 comments:

Post a Comment