Responsive Ads Here

Thursday, January 3, 2019

Jawabin Godiya!

GABATARWA:

Da sunan Allah Mai rahma, mai jin kai. Alhamdulillah muna qara godewa Allah (swt) a bisa ga irin ni'imomin da yayi mana. Tsira da aminci Allah su qara tabbata ga fiyayyen halitta annabi Muhammad (s.a.w) da iyalan gidansa tsarkaka.

Muna qara godewa Allah (swt) wanda cikin ludufinsa da yardassa ya nufemu da bude wannan application din mai tarin albarka, wanda kuma acikinsa Yana dauke da bayanai akan ita wannan shagon magani mai suna a sama wato DOM-DOMTY MEDICINE STORE, tare kuma da bayanai akan magun-guna daban-daban gamida fadakarwa akan wasu hanyoyi da za'abi domin prevention wato kariya daga cutuwar jika gaba daya.

Sannan a qarshe Munna godiya ga babban yaya kuma jigo a wannan a wannan katafaren shago shine Alh. Adamu Hassan (Ba matsala) wanda ya taimaka sosai matuqa gaya, muna fata Allah ya saka masa da alkairi.

Sai kuma qaninshi Alh. Salisu Hassan (wanda shima ya dauke da nashi katafaren shagon maganin a kusa damu.) Muna masa fatan alheri shima Allah ya taimaka.
Sai Kuma babban oga wato managing director na wannan katafaren shago Wanda gaba daya wannan application din take magana akai, shine Alh. Abdullahi Hassan, muna fatan Allah ya taimakeshi ya qara masa budi da wadata da arziqi mai albarka.

Ba zan manta da mayan yaran shagon namuba, irin manajan kasuwar kauye wata Abbakari (P.A na Bamatsala), sai kuma Sagiru, Mustapha da kuma Hassan.
Muna fatan Allah ya taimaki wannan shago ya kuma qara daukakashi Amin!



Uhm! 
....baza mu manta da Auwal Sufi ba acikin wannan hidimar, kazalika da kuma dan aikan shago wato Sale Ozil.

0 comments:

Post a Comment