Responsive Ads Here

Tuesday, April 21, 2026

Gyembon Cikin Baki

 Canker Sore (Gyembon Baki)


Canker sore: itace gyembon baki, kurji ne yake fita a baki, mafi yawa yana somawa ne da dan karamin kurji mai zafin gaske, wanda yakan iya fitowa a kowacce bangare na baki.



Alamomin Canker Sore sun hada da:

=> Farin kurji a baki

=> Ciwo mai tsanani

=> Wani lokocin yana zama jaa.

=> Yana zuwa da zazzabi


Mutum zai iya daukan Canker sore ta Hanyar Sunbatta/kiss ?


Mafi yawan canker sore bata yaduwa ta hanyar mu'amala ko kiss sai dai kadan daga cikin su, kuma hakanan yana warkewa da kansa ko ba'asha magani ba cikin kwana uku zuwa hudu.


Me yake kawo matsalar Canker Sore ?


1- Karancin sinadaran Vitamin B12, Zinc da folate a jiki yakan iya kawo matsalar Canker score.


2- Jin rauni a baki lokocin goge baki yakan iya kawo wannan matsalar.


3- Allergy: Idan garkuwar jiki ya kyamaci wata kwayar bakteria ko abinci yakan iya kawo wannan matsalar.


4- Mata suna fuskantar wannan matsalar lokocin al'ada ta dalilin rikicewar sinadaran hormones.


5- Yawan damuwa (stress) yakan iya kawo wannan matsalar.


6- Kwayar cutar bacteria Wanda akafi sani da H-pyloria yana kawo wannan matsalar.


7- Haka Kuma wassu cututtaka kamar:

   => Chrons disease

   => Irritable bowel syndrome

   => ulcerative colitis

   => HIV da sauaran su sukan iya kawo wannan matsalar.


Yadda za'a magance wannan matsalar a lokocin da ya fito:


1- A sa gishiri/manda chokoli guda cikin ruwa kopi daya mai zafi a kurkure baki da shi safe da yamma.


2- Ko kuma a sa bakin soda chokoli guda cikin ruwa kopi daya mai zafi a kurkure baki da shi a kalla lokoci uku a rana.


3- Bayan haka a samu zuma mekyeu a shafa a  wajen a kalla lokoci hudu a rana ( zuma na dauke da sinadaran kashe kwayar cutar bakteria da kuma sinadaran rage kuburi da radadi).


4- Idan ba'a samu zuma mekyeu ba za a iya amfani da man kwakwa shima lokoci uku zuwa hudu za'a shafa a wajen.


5- Za'a iya hadawa da Kwayar vitamin B complex a kalla so daya zuwa biyu a rana.


=> Daganan idan babu alamar sauki cikin kwanaki biyu zuwa 3 a garzaya zuwa Asibity a sanan ta bincike a gano me ya kawo matsalar.


=> Kada ayi amafani da lemun tsami ana gogawa wajen domin yana tsananta ciwon maimakon warkar wa.


Dom-Domty Medical Tips 

via-the2brothers-links

Saturday, January 17, 2026

'Ya-'Yan Dabino

 Abinda mafi yawan mutane ke watsarwa anan nigeria a matsayin shara, a wasu ƙasashe ana kallonsa a matsayin zinariya. Ɗaya daga cikin irin waɗannan abubuwa shi ne kwallon dabino. 

Wannan dai kwallon dabinon da kake jefarwa bayan kaci dabino, shine tushen wani kasuwanci mai ban mamaki da ake kira Tooth Powder (garin tsaftacce hakora).

Garin tsaftace hakora ko kuma kace Tooth Powder da ake yi daga kwallon dabino da aka sarrafa zuwa Activated Charcoal ba sabon abu ba ne a duniya, a zahiri shi ne tushen yawancin black toothpaste da kake gani ana siyarwa da tsada a kasuwa.

Kuma abin birgewa zaka iya hada irin wannan garin hoda din na kwallon dabino a gida da kayan aiki masu sauƙi, ba tare da manyan injuna ba. 

Da farko, ya kamata mutum ya fahimci me yasa kwallon dabino ke da amfani ga hakori, kuma yake da kyau ayi amfani da shi wurin brush na hakori ko tsaftace hakora. Kwallon dabino idan aka kona shi a hanya ta musamman, yana zama charcoal mai tsabta sosai wanda ke da ikon cire datti da tarkacen abinci da ya makale a hakora, haka zalika yana rage warin baki, yana taimakawa wajen rage irin rawayar nan da zaka gani a hakoran wasu, yana hana yawaitar ƙwayoyin cuta a baki. 

Wannan shi ne dalilin da yasa Tooth Powder na charcoal yake da kasuwa sosai a kasuwanni, musamman a tsakanin matasa da masu son organic & chemical-free products.

Yadda ake fara hadawa daga farko har karshe, mataki na farko shi ne zaka nema ko kafara tara kwallon dabino, ana iya samun sa kyauta a wuraren sayar da dabino ko wurin da ake sarrafa dabino, idan ma siye zakayi ba shi da tsada kwata-kwata. Bayan ka tara shi, sai ka wanke kwallon dabinon sosai domin cire yashi da dattin dake jikinsa, sannan sai ka saka shi a rana domin ka busar da shi gaba ɗaya a rana.

Bayan ya bushe sosai, sai a shiga mataki na biyu wanda shi ne kona kwallon dabinon, amma a nan akwai abu mai muhimmanci da zaka lura dashi, ba'a kona shi kamar itace da wuta mai iska sosai ana kona shi ne a cikin tukunyar ƙarfe ko wani abu mai kama da hakan domin ya zama charcoal mai tsabta (activated charcoal) ba toka ba, kona kwallon dabino yana ɗaukar lokaci amma shi ne ginshiƙin ingancin Tooth Powder ɗinka, don haka karkayi garaje. 

Da zarar ya koma charcoal, sai a bar shi ya huce gaba ɗaya, daga nan sai a shiga mataki na uku wato bangaren nikawa da tacewa, a nan, ana nika charcoal ɗin sosai har sai ya koma gari mai laushi kamar fulawa. Ana tace shi da kyalle ko sieve domin cire datti da manyan burbushin kwallon dabinon, domin Tooth Powder dole ne ya zama mai santsi sosai saboda kada yaji ma hakori ciwo. 

Mataki na gaba shi ne haɗawa da wasu kayan na musamman domin ya zama cikakken Tooth Powder. A nan idan ka kawo garin charcoal dinka na kwallon dabino da ka kammala aikinsa sai ka nemi garin kanumfari kaɗan (antibacterial) sai kuma garin mint ko peppermint (domin ɗanɗano da ƙamshi) sai ka samu baking soda kaɗan (domin whitening na hakori) duka wadannan ana haɗa su ne daidai gwargwado, ba tare da an cika wani ba musamman baking soda kar a cika ta sosai, domin kada ya cutar da enamel na hakori, bayan an gauraya su sosai, daganan Tooth Powder dinka ya kammalu In Sha Allah. 

Mataki na ƙarshe shi ne a samu robobin da za'a zuba a ciki ayi amfani dasu wurin siyarwa, ana saka Tooth Powder a cikin kwalba ko roba mai murfi sosai, sannan a rubuta sunan kaya da yadda ake amfani da shi. 

100%, mutum zai iya yin Tooth Powder a gida. Ba sai kana da factory ba, abin da ake bukata shi ne tukunya domin kona kwallon dabino, turmi da tabarya ko injin nika domin mayar dashi gari sai kuma sieve ko kyalle domin tacewa daganan sai kwalabe ko robobi na zubawa.




Hanyoyi Don Kula da Lafiyar Baki da Haƙora 


Samun lafiyayyun haƙora na buƙatar kulawa ta tsawon rayuwa. Ko da ana ce maka haƙoranka suna da kyau, wajibi ne ka rika ɗaukar matakan da suka dace a kullum domin kare su daga matsaloli. Wannan ya haɗa da amfani da kayan kula da baki masu kyau da kuma kiyaye halayen yau da kullum.


1- Kada ka kwanta bacci ba tare da ka goge haƙoranka ba.

Shawarwarin masana shi ne a goge haƙora aƙalla sau biyu a rana. Goge haƙora kafin kwanciya bacci yana kawar da ƙwayoyin cuta da datti (plaque) da suka taru a baki tsawon yini.


2- Kada ka yi watsi da harshe.

Datti (plaque) na iya taruwa a kan harshe ma. Wannan na iya haddasa wari a baki, kuma har ma ya jawo wasu matsalolin lafiyar baki.


3- Ka ɗauki amfani da zaren tsabtace haƙora (floss) da muhimmanci kamar goge haƙora.

Mutane da yawa suna goge haƙora amma su yi watsi da floss. Floss ba wai kawai don cire ragowar abinci tsakanin haƙora ba ne, yana kuma:


~ motsa dadishi (gums),

~ rage taruwar datti,

~ da rage kumburi a bakin haƙora.


4- Ka yawaita shan ruwa.

Ruwa shi ne abin sha mafi alheri ga lafiyar jiki gaba ɗaya, har da lafiyar baki. Yana taimakawa wajen wanke baki da rage yawan acid da ƙwayoyin cuta.


5- Ka rage cin abinci mai zaƙi da mai tsami (acidic).

Zaƙi yana rikidewa ya zama acid a baki, wanda ke lalata murfin haƙora (enamel). Wannan ne ke haddasa ramukan haƙora (cavities).

Haka kuma, ’ya’yan itatuwa masu tsami, shayi da coffee na iya rage ƙarfinsa enamel idan aka yawaita.


© via-the2brothers-links