Abinda mafi yawan mutane ke watsarwa anan nigeria a matsayin shara, a wasu ƙasashe ana kallonsa a matsayin zinariya. Ɗaya daga cikin irin waɗannan abubuwa shi ne kwallon dabino.
Wannan dai kwallon dabinon da kake jefarwa bayan kaci dabino, shine tushen wani kasuwanci mai ban mamaki da ake kira Tooth Powder (garin tsaftacce hakora).
Garin tsaftace hakora ko kuma kace Tooth Powder da ake yi daga kwallon dabino da aka sarrafa zuwa Activated Charcoal ba sabon abu ba ne a duniya, a zahiri shi ne tushen yawancin black toothpaste da kake gani ana siyarwa da tsada a kasuwa.
Kuma abin birgewa zaka iya hada irin wannan garin hoda din na kwallon dabino a gida da kayan aiki masu sauƙi, ba tare da manyan injuna ba.
Da farko, ya kamata mutum ya fahimci me yasa kwallon dabino ke da amfani ga hakori, kuma yake da kyau ayi amfani da shi wurin brush na hakori ko tsaftace hakora. Kwallon dabino idan aka kona shi a hanya ta musamman, yana zama charcoal mai tsabta sosai wanda ke da ikon cire datti da tarkacen abinci da ya makale a hakora, haka zalika yana rage warin baki, yana taimakawa wajen rage irin rawayar nan da zaka gani a hakoran wasu, yana hana yawaitar ƙwayoyin cuta a baki.
Wannan shi ne dalilin da yasa Tooth Powder na charcoal yake da kasuwa sosai a kasuwanni, musamman a tsakanin matasa da masu son organic & chemical-free products.
Yadda ake fara hadawa daga farko har karshe, mataki na farko shi ne zaka nema ko kafara tara kwallon dabino, ana iya samun sa kyauta a wuraren sayar da dabino ko wurin da ake sarrafa dabino, idan ma siye zakayi ba shi da tsada kwata-kwata. Bayan ka tara shi, sai ka wanke kwallon dabinon sosai domin cire yashi da dattin dake jikinsa, sannan sai ka saka shi a rana domin ka busar da shi gaba ɗaya a rana.
Bayan ya bushe sosai, sai a shiga mataki na biyu wanda shi ne kona kwallon dabinon, amma a nan akwai abu mai muhimmanci da zaka lura dashi, ba'a kona shi kamar itace da wuta mai iska sosai ana kona shi ne a cikin tukunyar ƙarfe ko wani abu mai kama da hakan domin ya zama charcoal mai tsabta (activated charcoal) ba toka ba, kona kwallon dabino yana ɗaukar lokaci amma shi ne ginshiƙin ingancin Tooth Powder ɗinka, don haka karkayi garaje.
Da zarar ya koma charcoal, sai a bar shi ya huce gaba ɗaya, daga nan sai a shiga mataki na uku wato bangaren nikawa da tacewa, a nan, ana nika charcoal ɗin sosai har sai ya koma gari mai laushi kamar fulawa. Ana tace shi da kyalle ko sieve domin cire datti da manyan burbushin kwallon dabinon, domin Tooth Powder dole ne ya zama mai santsi sosai saboda kada yaji ma hakori ciwo.
Mataki na gaba shi ne haɗawa da wasu kayan na musamman domin ya zama cikakken Tooth Powder. A nan idan ka kawo garin charcoal dinka na kwallon dabino da ka kammala aikinsa sai ka nemi garin kanumfari kaɗan (antibacterial) sai kuma garin mint ko peppermint (domin ɗanɗano da ƙamshi) sai ka samu baking soda kaɗan (domin whitening na hakori) duka wadannan ana haɗa su ne daidai gwargwado, ba tare da an cika wani ba musamman baking soda kar a cika ta sosai, domin kada ya cutar da enamel na hakori, bayan an gauraya su sosai, daganan Tooth Powder dinka ya kammalu In Sha Allah.
Mataki na ƙarshe shi ne a samu robobin da za'a zuba a ciki ayi amfani dasu wurin siyarwa, ana saka Tooth Powder a cikin kwalba ko roba mai murfi sosai, sannan a rubuta sunan kaya da yadda ake amfani da shi.
100%, mutum zai iya yin Tooth Powder a gida. Ba sai kana da factory ba, abin da ake bukata shi ne tukunya domin kona kwallon dabino, turmi da tabarya ko injin nika domin mayar dashi gari sai kuma sieve ko kyalle domin tacewa daganan sai kwalabe ko robobi na zubawa.
Allah yasa mu dace.
© via-the2brothers-links








0 comments:
Post a Comment