Responsive Ads Here

Friday, February 15, 2019

Saurara ka karanta

MUHINMANCIN GWAJI KAFIN AURE.



Gabatarwa:

Yin gwaji kafin aure yanada matukar muhimmanci sosai, dahakane za'a gujewa kamuwa da cutukan da ake samu bayan an yi AURE, akwai cutuka kala-kala wadanda ake samun su sakamakon rashin yin gwaji kafin ayi aure, irin su cutukan da ake gado daga wajen iyaye ko kuma ake samun su ta hanyar saduwa ko kuma ta hanyar hada jiki da wan da yake da cutar.

Dan haka ina mai bawa yan uwa shawara da a din ga yin gwaje-gwaje kafin ayi aure, ta haka ne xa'a iya kaucewa wadansu cutukan da mutum yake dauke da su, wata kilama bai san yanada su ba.
 kaga ya taimaki kansa kuma ya taimaki auransu.

Idan kalar cutar wacce za'ayi maganinta ne kaga sai ayi maganinta kafin suyi aure yawarke.



Kalar Cutukan Da Akeyin Gwaji Kafin Ayi Aure:

1-  Sickle cell

2-  HIV

3-  Hypertitis

4-  Gonorrhea, e.t.c
           
1- Sickle Cell: is a condition usually cause of abnormality in structure of haemoglobin.

Ma'ana wata cuta ce wadda yawanci take haifarda rashin cikar halittar jini.
wato  a yadda halittar jinin yake to ya sami tawayar cikar structure dinsa.



NOTE/AKULA: 

Wadannan cuta gadarta ake yi daga wajan iyaye sakamakon canjin yanayin kalar jinsi a tsakanin UWA da UBA, ana samunta ne idan kalar jinin uwa ko uba ya xama kamar haka:

1-  AS - AS
2-   SS - AS
3-  AS - SS
4-   SS - SS

Dukkansu wadannan misalan akwai yiyuwar a sami mai sikila.



Yanayi Hali Da Mai Wannan Sikila Yake Shiga:

1- Matsanancin ciwon gaba (joint pain).

2- Karanci jini.

3- Karancin ruwa a jiki.

4- Faduwa (shock).

5- Matsalar al'ada.

6- Yawan barin ciki.

7- Kunburin yan yatsa da hannaye.

8- Lokacin sanyi da kuma zafi yana shan wahala sosai.
e t.c

Yanayin Da Mai Sikila Yake Shiga Idan Abin Yayi Tsanani Sosai:

1- Mutuwar mata masu dauke da juna biyu.

2- Yawan barin ciki.

3- Ciwan zuciya.

4- Rashin saurin girman jiki.

5- Rashin nauyin jiki.
etc

Abubuwanda Da Suke Sawa Ya Shiga Matsanancin Hali:

1-  Drinking alcohol ~ shangiya.

2-  low oxygen tension ~ karancin shakar iska.

3-.  pregnancy ~ juna biyu.

4- Matsananciyar damuwa ~ yawan damuwa.

5-  Cold weather and hot weather ~ yanayin sanyi ko zafi.

6-  Infection ~ kwayar cuta.


Ana bawa mai dauke da wannan ciwo shawarwari akan:

1.  Idan yanayi sanyi yazo, suke amfanida abubuwan da xai ragemusu jin sanyi.

2.  idan yanayin zafi yazo, suke samun gundayake da iska.

3.  suke shan maganinsu akan bisa ka,ida.

4 .  kuma sukecin abubuwa masu karin jini, da gina jiki.

5  kuma dole sai ana lura da mai dauke da wannan cuta , akodayaushe.
etc

Shawarinda Likitoci Suka Bayar:

✓ Jini mai cikarkiyar lafiya shine wanda jininsa yake AA.

✓ Jinin mai AS kuma lafiya lau amma kuma yanada alamar dauke da cutar idan ya auri AS irinsa zasu haifi mai irin wannan cutar , amma mix zasu dingayi.

✓ Daman abinda yaka mata mai AA ya auri mai SS sabida bazasu haifi mai dauke da wannan cuta ba, saidai su haifi , mai alamar dauke da cutar.

✓ Bai kamata mai SS da mai  SS su auri junaba. Sabida gabadaya yaransu suma zasu kamu da cutar.



Wadanda ya kamata ace aure zai yiwu tsakaninsu ba tareda matsla ba:

AA - AA
AS - AA
AA - AS
AA -  SS

Masu jini kalar haka zasu iya yin aure ba matsala.

Wadanda idan suka yi za a sami matsala kuma sune:

SS - SS
AS - AS
AS - SS

Duk masu jini kalar haka bai kamata  su yi aure ba da  akwai matsala sosai.


Wasu na ganin idan mai wannan cutar ya kai shekara 25 cutar ta kan rabu da shi, Amma ga abinda likitoci suka fadi:

Barabuwa da ita yakeba, kawaidai, kasan garkuwar jikin babba da yaro akwai banbancin, ta yaro batada karfi sosai. Amma ta babba tanada karfi sosai.

Abinda ake nufi da garkuwar jiki shine:

Akwai wasu sinadarai acikin jikin mutum  wadanda, Allah ne yasanyasu, dan suyi fada  da cuta idan tashigo jikin mutum.

Abunda yasa yaro yafi shan wahalar cutar shine, nayaro basuyi kwariba kamar na babba.

Ance wannan cutar a bargo take kuma Ance ana iya kwashe bargo a sanya wani transplant, Shin da gaske ne?

To anamma ga abinda likitoci sukace:

Da gaskene ammafa da akwai yuyuwar yadawo, kuma ga tsada akalla yakai kusan million 20 koma fi. kuma banan kasar akeyiba.



✓ To bisa ga bayananda mukayi a sama zaku fahimci cewa , rashin zuwa gwaji kafin aure , akwai matsala mai tarin yawa.

✓ Ya kamata mutane su fahimta, gwajin nanfa bafa wani abune mai wahalaba, cikin dan wani karamin lokaci angama.

✓ ku fahimci wani abu zakuga dukkan maras lafiya dake dauke da wannan cuta , zakuga iyayan masu wannan kullum hankalinsu ba a kwance yakeba, sabida akoda yaushe cutar zata iya tashi.



....Insha Allah, zamu kawo muku bayanan nan gaba.



via: Dom-Domty Medical Tips



0 comments:

Post a Comment