Responsive Ads Here

Sunday, January 26, 2020

FADAKARWA:

LASSA FEVER


Lassa fever ( haemorrhagic fever) : cuta ce da akan dauketa ta hanyar idan abinci ko abin sha ta gurbata da fitsari ko kashin bera irin ta jeji, kwayar cutar Lassa Virus ce take kawo shi.

Sauran hanyoyin kamuwa da cutar sun hada da cudanya da wanda ke dauke da cutar.

Haka kuma jami'a da mai dauke da cutar na iya jawo wannan cutar ta Lassa fever.

Bayan mutum ya kamu da cutar alamomin cutar kan fara bayyana daga kwanaki biyu zuwa mako uku.


ALAMOMIN LASSA FEVER

Kamar yadda babbar hukumar lafiya ta Duniya (WHo) tafitar alamun kamuwa da cutar sun hada:

1- Zazzabi mai zafin
2- Amai
3- Gudawa mai jini
4- Fidda jini ta kafofin jiki.


HANYOYIN KARIYA :

1- Kada ayi amfani da abinci wanda za'aci ba tareda sai an wanke ba kamar su garin kwake.

2- Duk matar da ba'a yarda da tsaftar ta ba a kauracewa abincin ta .

3- A kiyaye tsabtar muhalli da abinci da ake amfani da ita .

4- A rufe duk wani abinci da abin sha da aka ci aka rage kuma a dumama shi kafin asake amfani.

5- Kada aci kayan Lambu  Irin su salat wanda ba dafasu akeyi ba ,sai an wanke da ruwan manda .

6- Wadanda wannan cutar ta kamasu a kyebesu da haduwa da wassu jama'a.

7- A tabbatar an tace sannan a tafasa ruwan da aka debo daga rafi ko rijiya kafin a sha .

8- A tabbata an wanke hannaye da sabulu kafin cin abinci da bayan cin abinci.

9- Wandan da suka kamu da wannan cutar kuma suka warke a hakura da jima'i na tsawanni sati 2 zuwa wata Daya.

10- Idan akaga wadannan alamomin ayi gaggawa akai mara lafiya zuwa asibity.

11- Anemi shawarwarin likitofi kafin ayiwa gawa wanka wanda yamutu da wadannan alamomin.




PUBLIC ANNOUNCEMENT.  

Take/report any person with the following symptoms to the nearest health facility/hospital: 

1. High grade fever
2. Bleeding from especially nose and ears
3. General body weakness/muscle pain
4. Malaise
5. Headache
6. Sore throat  Ensure personal and environmental hygiene.


Haemorrhagic fevers (e.g. Lassa fever and Ebola fever) are real. 


May God save us all.

Signed: 
thë2ßrøthêrs

0 comments:

Post a Comment