Responsive Ads Here

Thursday, February 6, 2020

'Yar Wuya/Beli

CIRE YAR WUYA DA KUMA BELI A JARIRAI. 

....Abisa duba ga wasu daga cikin al'adunmu na Hausawa, Hakan yasani wasu 'yan nazarce- nazarce wanda har a qarshe ya kaini ga yin rubutu Akan maudu'in dake a sama, tare kuma da Kokarin samo amsoshin wasu tambayoyi da nayi kamar haha:

 Shin hakan yana da wani fa’ida a likitance? Duba da irin yanda yaran ke shan wahala bayan cire mu su. Me yasa ake cirewa? Sannan me zai faru idan ba’a cire ba?! 

A mahanga ta likitanci cire wadannan abubuwan ba shi da wani fa’ida (medical benefit), sai dai ma ayi batun illa. Sannan duk dalilan da aka kawo na cirewar (ga masu cirewa kenan) idan mutum ya yi nazari, zai ga cewa ba su bayar da wata ma’ana ba.

A addinance kam akwai ‘controversies’ da yawa akan abun. Wasu Malaman sun tafi akan cewa wajibi ne a cire, wasu kuma sun ce yana da kyau a cire (amma ba wajibi ba), wasu kuma sun dauki matsayar cewa kar a cire.


A zahiri dai, ya fi kama da al’ada kawai, wacce ta fi shahara a kasar Hausa. Kuma kamar yanda muka sani, akwai al’adu da yawa wadanda suke cutarwa (Harmful Traditional Practice) ga lafiyar mutum, amma ana yin su. Cire ‘yar wuya da kuma beli sun fado cikin misalan wadannan al’adun; wankan jego da tafasasshen ruwa, shan kunun kanwa wanda ya wuce qa’ida ga mata masu juna biyu/ masu shayarwa, yin shayi/kaciya ga mata, dss; na kadan daga cikin wadannan al’adun.



- MENENE BELI? 

Shi ‘Beli’ sunan shi “Uvula” a likitance. Shi ne ya rufe tsakanin baki da makogoro.. (Da yake likitanci ba da Hausa ake koyar da shi ba, wasu lokutan sunayen kan iya canjawa ‘depending’ on yankin da mutum ya ke).

Babu wani ‘Medical benefit’ na cire shi a jikin jariri gaskiya. Wadanda suke cirewa sun yi ‘theorizing’ cewa yana hana gudawa da amai (amma ba su yi bayanin ya hakan ke faruwa ba), yana kawo shakewa idan ana shayar da jariri, sannan kuma wai saboda tsoron kar ya kumbura idan cuta ta kama shi.

Amma kuma illar cire shi ya fi yawa. Kama daga ballewar jini, da kuma kassara ‘normal anatomical presentation’ na bakin mutum, yiwuwar wucewar abu daga bakin mutum zuwa cikin hancin shi, da kuma daga baki zuwa huhu idan jariri, dss.

Babu wani dalili da zai sanya a cire ma jariri Beli matukar ba wai yanayi ya bada hakan ba ne, kamar misali kamuwa da wata cuta, dss.




- MENENE 'YAR WUYA? 

Kamar yanda nace Hausa na bambanta. Wasu na kiran shi hakin wuya, wasu kuma ‘yar uwa. Kila a wani wajen ana kiran shi wani abu ne ma daban.

Shi kuma ‘yar wuya shi ne “Palatine tonsil” [wannan shi aka fi cirewa, kuma shi ya fi hadari]. Saboda ko ba komai su “tonsils” generally kamar misalin barikin sojoji ne a kasa, inda ya ke tattara sojoji ya basu horo. A cikin ‘tonsils’ ne ake samun ‘immune cells’ [wadanda kamar su ne sojojin jikin mutum da ke yaqi da cututtuka] da ke kare jiki daga kamuwa da wasu kwayoyin cututtuka. Ka ga idan aka cire shi (tonsil) daga jikin mutum, zai zama kamar an cire sojoji daga kasa ne a lokacin yaqi ko?

Duk wata kwayar cuta da ta shiga bakin mutum kafin ta je makogoro, sai wadannan “Palatine tonsils” din [su ne kuma ake ce ma ‘yar uwa] sun tare ta, sun yaqe ta domin su hana ta wucewa. Idan babu kai tsaye zata wuce zuwa makogoro kenan; daga nan kuma sai inda Allah Ya yi. Akwai shi kan shi makogoro, akwai ciki, akwai hanji, akwai hanta, akwai huhu; duk cuta zata iya zuwa musu daga baki.

Binciken likitoci ya tabbatar da cewa, jariran da ake cire ma ‘yar wuya din nan sun fi kamuwa da cututtuka fiye da wadanda ba’a cire musu ba. Musamman cututtukan da suka danganci baki, hanci da kuma makogoro.

Akwai yanayin da zai iya bayar da cewa a cire din, misali idan suka kamu da cuta suka kumbura da kuma barazanar yada cutar zuwa wani sashe daban na jikin mutum. Ana cirewa, ba su kadai ba ma; har sauran “tonsils” ana iya cirewa idan yanayin cuta ya bada. Amma idan babu wani dalili, sam bai kamata ake cirewa jarirai ba.




A takaice dai ba shi da wani fa’ida a likitance cire wadannan abubuwan. Kowanne daga cikin su yana da amfani a jikin jariri. Jikin dan Adam shi ne cikamakon halitta, duk abun da ka ga Allah (T) Ya halitta a jikin dan Adam, akwai amfanin shi. 

Allahu a’alam..


          >>>>> Yours Dom-Domty <<<<<


....Ku Kasance da shafin Dom-Domty a Koda yaushe, domin samun bayanai da fadakarwa da suka shafi harkar kiwon lafiya!




   Sannan Angaida Yara Manyan Gobe!




Signed:
thë2ßrøthêrs

1 comment:

  1. Best I’ve read, simple and apprehending article.

    Thank you Author.

    ReplyDelete