Responsive Ads Here

Saturday, August 1, 2020

Happy Juma'a & Eid Mubarak!

Taqabbalallahu Minna wa Minkum!

Favour of Allah is limitless and unlimited, His grace is immeasurable, His power has no boundary. May his endless blessing be showered on you forever!
During this special day, Allah replaced Isma'il with a Ram for prophet Ibrahim. May He replace your sorrow with joy, happiness, love, warmth and good health.
Wishing that Allah accepts your good deeds and sacrifices, alleviate your suffering and forgives your transgressions!

Sunday, June 28, 2020

Lafiya Uwar Jiki....

HANYOYIN KARA LAFIYA DA GINA JIKI:


Lafiyar jiki abu ne da kowa ke bukata domin kuwa masana kiwon lafiya sun yi kididdiga akan cewa, da yawa daga cikin cututtukan dake kama jikin dan Adam su na bayuwa ne dangane da irin cimarsa.
Idan mutum ya kauracewa da yawa daga cikin nau'ukan abinci da ake sarrafasu a kamfanunnka, kama daga kifin gongoni zuwa lemuka na gongoni, to tabbas zai tsarkeke lafiyar jikinsa daga sunadaran calories.
Wannan sunadaran na calories su na da tasiri kwarai da gaske wajen karya garkuwar jikin dan Adam, domin kuwa su na jefa sassa daban-daban na jikin dan Adam cikin hadarin kamuwa da cututtuka.


Ga jerin hanyoyi 6 da za su kara habaka lafiya da gina jikin dan Adam:

1. Yawaitar amfani da kayan hatsi irinsu; gero, dawa, acca, masara, uwa uba alkama, domin kuwa su na kara karfafa karfin jikin dan Adam da kuma bayar da kariyar cututtuka irinsu, ciwon zuciya, ciwon sukari da kuma ciwon daji.
2. Amfani da 'Ya'yan itatuwa da ganyayyaki:
3. Rage amfani da gishiri da kuma sarrafaffen sukari.
4. Ana bukatar mutum ya yawaita shan ruwa domin masana kiwon lafiya sun bayyana cewa ruwa ba ya taba yin yawa a jikin dan Adam saboda irin bukatuwar jiki ga ruwa.
5. Kauracewa barasa da sunadarin Caffeine, wannan sunadarin ana samun shi a cikin lemo na Coca Cola da kuma Nescafe.
6. Rage amfani da nama da kwai na kajin gidan gona, domin kuwa sinadaran gina jikinsu ba daya yake da kajin hausa ba. Saboda haka ga mai bukatar sunadarin Protein a jikinsa, akwai irinsu gyada, gujjiya da kuma wake da suke kunshe da wannan sinadarai.


....wannan rubutu dai saboda Sufi akayishi bisa ga la'akari da himmarsa, karamarsa, gami-da.......
Tafiyayyune kawai zasu gane sauran batun, banda waigaggu!



Signed:
thê2brøthërs

Ciwon Baya/Back pain

Barkan mu da warhaka, A yau zamuyi batune Akan:
 CIWON BAYA (backache/Back pain) 


Kafin mu san mene ne ciwon baya da yadda yake aukuwa, ya kamata mu san ya shi gadon bayan yake. Gadon baya: ya hada da sandar kasusuwan baya, da wasu fayafayin da suke tsakankanin su kasusuwan, sai kuma naman da ya lullube shi, da kuma jijiyar laka ta gadon baya da ke cikin shi sandar kashin. Dukkanin wadannan abubuwa da aka lissafa wato da lakar, da kashin da tsokar duk zasu iya jin ciwo, susa ciwon baya. Kuma ana jin ciwon ne a tsakiyar baya daga kasan hakarkari (awazzu) zuwa kugu, domin duk zafin da akaji a gefe ko kwibin wannan wuri ba sunan shi ciwon baya ba, watakil koda ce ko wani abun daban.


 Ciwon Baya (Back pain):- ba karamar matsala ba ce, domin kusan a kullum sai anje asibiti a kanta. Kusan an kiyasta cewa kowane mahaluki zai samu (ko ma ya taba samun) ciwon baya ko da sau daya ne a rayuwa, a wasu da dama kuma ya zauna yaki tafiya. Mukan samu ciwon baya ne yayin da muka dauki abu mai nauyi, ko muka buge, ko muka murda bayan da karfi ba tare da mun sani ba, kamar a fagen wasanni ko wata cuta ta taba shi. (I.Y.Y.) YAWAN FITSARI (Polyuria)!!!
Akwai abubuwa da dama da kan iya kawo yawan fitsari, tun daga canjin yanayi, zuwa yawan shan ruwa ko kayan shaye-shaye, zuwa samun juna biyu zuwa rashin lafiya zuwa magunguna. Yawan fitsari na faruwa yayin da mutum ya ga cewa yawan zuwa makewayinsa domin fitsari ya karu, ko yawan fitsarin da ke zuba ya karu ko da ba samu karuwar zuwa bayan-gidan ba. Canjin yanayi daga na zafi zuwa na sanyi zai iya kawo yawan fitsari. Yawa a nan na nufin zubar fitsari mai yawa ba kadan ba. Yawan shan abubuwa masu ruwa ma kan iya kawo irin wannan yawan. Mai juna biyu ma da ya fara girma za ta rika jin fitsari a kai-akai saboda mahaifa na danno mafitsara. Sai Rashin lafiya. Ana ganin shigar kwayoyin cuta mafitsara kan iya sa yawan fitsari, amma a nan yawan na nufin yawan jin fitsarin, don ko an je ba a ganin yana zuba da yawa. Wani ciwo mai kawo irin wannan alama kuma shi ne na kumburin prostate a maza wadanda suka manyanta. Sai matsalar ciwon suga, wadda ita kuma za ta iya kawo yawan yin fitsari a kai-akai, kuma mai yawa ba kadan-kadan ba. Sai matsalar ciwon koda, ita ma za ta iya kawo yawan fitsari kafin daga baya ya dauke a wasu lokutan. Daga karshe sai wasu magunguna. Magungunan da akan ba wasu wadanda ruwa ya taru a jikinsu kamar masu hawan jini misali ko masu ciwon hanta, kan iya sa yawan fitsari. Akwai wasu na gargajiya ma wadanda mutum kan saya ya sha haka nan a titi, su ma za su iya kawo yawan fitsari. Don haka duk wanda yake da alamomin yawan fitsari ba na canjin yanayi ko na shaye-shaye ba yana da kyau ya je a duba shi, in ta kama ma a yi masa gwaje-gwaje don a tantance matsalar.


ME YAKE KAWO CIWON BAYA? 

Abubuwan da kan kawo ciwon baya sun hada da: 
1. Yawan shekaru: Wato girma ko tsufa. Wannan shi ne kan gaba wajen kawo ciwon baya, domin da wuya yara suyi. An fi ganin ciwon baya a dattijawa da tsofaffi wadanda bayansu ya riga ya fara rauni, ko kasusuwan suka riga suka fara zaizayewa saboda karancin ma’adinai irinsu Vitaman na rukunin D da Calcium. Don haka idan yawan shekaru ne ke kawowa mutum ciwon baya sai an hada da magungunan bitaman da motsa jiki ta hanyar gashi wato Physiotherapy kafin abin yayi sauki.

2. Sai kuma kiba: Wadda kan kara wa gadon bayan nauyi, ta yadda tsokar da kashin da kushin din duk za su kasa samun sakewa. Mai wannan matsalar idan ba rage kibar ya yi ba, ba zai daina samun matsalar ba komi magani.

3. Gado: Akwai kuma wadanda akan haifa da karkataccen kashin gadon baya, kamar kusumbi ko doro ko dai wani rashin daidaito na kashin bayan wanda kan iya sa yawan ciwon bayan. Shi wannan idan aka gano hakan ne, yawanci tiyata ake a mikar da lankwasar.

4. Yawan aiki a tsaye ko a duqe ko a zaune na tsawon lokuta, zai iya sa tsokar jikin kashin ta gajiya. Kai a wasu lokutan ma irin wannan kan iya sankarar da baya na dan wani lokaci. Yawan motsa jiki kan iya magance ciwon baya a masu irin wannan Yawan motsa jiki kan iya magance ciwon baya a masu irin wannan matsala.

5. Yawan daga kayan nauyi: Mutane masu aikin daga kayan nauyi sun fi kowa samun hadarin zamowar kushin din da ke tsakankanin kashin gadon baya. Idan mutum zai daga nauyi ko da ruwan wanka ne kada ya daga a duqe, sai daga tsugune. Don haka ne ma kuma ga masu sa leburori aiki su rika bin ka’idojin aiki, ta hanyar basu kayan daukar nauyi na zamani da inshorar lafiya ga wadannan.

6. Buguwa ta hatsari: Wadda zata iya kuje tsokar ko ta sa karayar kashin, ko ta sa kashin ya matse lakar, ko ta sa kushin-kushin din tsakankanin su zamo. Don haka idan mutum ya taba buguwa a baya yana cikin hadarin samun ciwon baya.

 7. Tsayi: An tabbatar da cewa wadanda suke da tsayi sosai sunfi sauran mutane yawan samun ciwon baya. Don haka idan kina da tsayi sosai za ta iya kasancewa shine.

8. Ciwon Sanyin kashi: Ga mai ciwon sanyin kashi wanda yafi kama yatsu da gabobin hannu ko na gwiwoyi, za a iya rashin dace ya tabo har gadon baya. Don haka ba abin mamaki bane mai ciwon sanyin kashi ya ji bayansa ya fara ciwo. A irin wannan magungunan sanyin kashin kan iya sawa na bayan ma ya lafa.

9. Yanayin Wurin Kwanciya: Da yake kwanciyar barcin dare na daukar lokaci mai tsawo a kowace rana, yanayin kwanciya kan iya sa ciwon baya. Mutumin da ke kwana kan tabarma ba daya yake da mai kwana kan katifa ba, kuma katifar ma kowa yasan hawa-hawa ce. Gadon baya bai cika son kwanciya a wuri mai tauri da laushi sosai ba, ya fi son tsaka-tsaki, wato katifa maras tauri sosai, kuma maras laushi sosai. Da yake kin ce sai lokacin kwanciya kike samun ta’azzarar ciwon ya kamata ki nemi irin wannan.

10. Ciwon TB: Ciwon tarin fuka na TB kan iya barin huhu (suhe) ya tabo kashin gadon baya. Bayan huhu dama wuri na biyu da akafi ganin ciwon (suhe) tarin fuka shine kan kashin gadon baya. Don haka ba abin mamaki bane mai tarin fuka ya ji ciwon baya. Ga mai tarin fuka wanda ke shan magani, duk lokacin daya ji ciwon baya kwana daya, kwana biyu ya ki tafiya dole ya je a duba bayan sosai. Ban da wannan kwayar cuta ta TB akwai wasu kwayoyin cutar da kan iya biyo jini ma su kama kashin gadon baya.

11. Ciwon Daji: A lokuta da dama masu matsalar ciwon daji kona ina ne kan samu ciwon baya, domin ciwon daji kan bi jini ya hau kan kasusuwa. Ciwon daji ko na nono kona bakin mahaifa ko na hanji ko na huhu, ko na mafitsara duk sun fi tafiya kashin gadon baya.

12. Al’ada da samun juna biyu da karin mahaifa: a wasu mata su kuma lokutan al’ada ne kawai kan kawo musu ciwon baya maimakon ciwon mara ko na kugu. Samun juna biyu ma idan cikin ya haura watanni biyar zai iya danne kashin gadon baya asamu jin zafi. karin mahaifa ma wato fibroid kan iya jawo irin wannan. Idan mutum nada ciwon baya matsananci, ya duba duk wadannan abubuwa da aka lissafa ya kasa gano dalili, kai ko da ya gano dalili, yana da kyau kuma ya ziyarci likita inda za a duba shi a bashi magunguna. Idan abun bai tafi ba, in son samu ne a je babban asibiti kamar asibitin kashi, inda za a fara yimasa hotunan baya na d-ray da ma na zamani irinsu MRI idan ta kama, da ma sauran gwaje-gwajen jini. A lokacin ne za a gano ainihin musabbabi matsalar kafin a zo maganar magunguna, a wasu lokutan ma maganar tiyata ce.
 Wannan shine Allah ya bamu alkhairan dake cikin wannan rana !


.....domin samun ingantattun maganin ciwon baya na kwarai kuma, sai a garzayo Shagon Dom-Domty (medicine store).....



Signed:
thê2brøthërs

Sunday, March 1, 2020

Happy Weekend (3)

Random Short Jokes Of The Day That Will Crack Your Ribzz





1. When I was in primary school, I never knew the Nigerian national anthem was in English language.
Back then, it used to be like: 

“Araiz oh compamshown

Najeriya skolobey

Tusa awa fadaslan

witlo an sley anfe

Dale bo of awahirosfa

Shaleba vi inves

Tusa tusa awa mayt

Worle shobon in frido

Pis an yuniti”

Hehehe, don’t laugh at me, I know u also sang it like that.


2. When we were growing up they used to tell us that education is the key🗝to success

Now we went to school, graduated, got the key? And only to find out that the government has CHANGED the padlock.




3. Beat a Nigerian kid, console him with biscuits, then ask him “who beat you”? He points 👉🏻at another person. 

That is how bribery and corruption started in Nigeria 🇳🇬?


4. I think my iPhone is not working, I press the home button and I'm still at school 
Hahahah!

5. Imagine you go to the drug shop to buy poison to kill your self,
But you still wait for your change.... Are you serious?

6. Arsenal is like a student with a beautiful handwriting. But false answer!

7. Once you are 25 years, So you don't have to set an alarm.... 
Your problems will wake you up!



8. Dear mosquitoes i know biting is your job, 
But is singing necessary ?

9. No matter how good love messages are they,
Can't be compared to a bank alert...

10. In Africa we dont change batteries...
We slap the Remote control until it starts to behave...🤣

11. You can't be born on February and be normal, 
The month itself is not complete

12. Women will always tell you that men can cheat and tell lies, but they seem to be forgetting that "What a man can do, a woman can do better" ...Guys are you with me??🤣

13. I remember back then in 1964, we were only 3 on Facebook...
Mr Mark Zuckerberg, Mr Bill Gates and Myself. 
...Until you guys joined😠

14. One day you will have enough money to enjoy and settle your bills and all these sufferings will end. 
Don't shout Amen, just go and work.

15. In English class, a teacher asked his student to assume they are in war and write an essay on their experiences; one student was sitting idle and the teacher walked up to him.
TEACHER: why are you not writing?
STUDENT: I was killed immediately after the war started!




....just for us to laugh small

A man was in a public transport, And wanted to see the reaction of others.... So he took his phone and dialed a number, place the phone to his👂ear, And said in a low tune:
Baby, i can't come to you today because I'm in the same public transport with your husband....
I will call you later okey?

All the men in the bus demanded,
"Excuse me mister man!!
I want to see the number you just called Right now, it is hot and heated in the bus......

Even the driver want to know the last number the man called!
Am still there separating the fight.....
That's why i have not been very active on this platform since morning!









Signed:
the2brothers

Thursday, February 13, 2020

Happy Weekend (2)

My Letter To Corona Virus:



Dear CORONA VIRUS,
I want to beg you in the name of the poor in Nigeria, please don't listen to the empty boasts of our Nigeria leaders. Our leaders don't know what the are saying. How can they say they are ready and prepared for you?

Abeg Sir, na lie, na slip of tongue. Just yesterday they said they have voted N680m to prepare for you, just imagine!! How much is that?

Sir, Look at how your Younger brother, Lassa Fever, is dealing with our people, your brother is already in 28 states of Nigeria unstoppable talk less of you.

Dear CORONA VIRUS, your birth place, China, with all her sophistications couldn't withstand your anger.
*China is overwhelmed,
*WHO is overwhelmed,
*Advanced countries are scared,
*Nigeria is boasting.
(Snails do not attend a meeting of Animals with horns).

Please in our poor country sake, don't come here, we can't handle you, we don't have the money, we don't have any hospital, no Power, we don't even have hand gloves and nose masks, our Doctors are afraid of you.
Our Government is joke.

Thank you sir






Signed:
thë2ßrøthêrs

Thursday, February 6, 2020

Kunne/Ear

CIWON KUNNE   



Ita kunne kanta an kasa shi bari uku (3) :
1- Outer ear -  wajen kunne .
2- Middle ear - Tsakiyar kunne
3- Inna ear - Cikin kunne .

Mafi yawan ciwon kunne da mutane suke complaining ciwon tsakiyar kunne ne (Otitis media) .


ME YAKE KAWO CIWON TSAKIYAR KUNNE :  

Yana daga cikin abubuwanda suke kawo ciwon tsakiyar kunne :
1- kwayar cututtuka kamar su :   
a- Bakteria   
b- Virus
 Amma mafi yawa bakteriya ne, wadannan kwayoyin cututtukan yawanci suna samun hanyar shiga ne ta makogoro zuwa tsakiyar kunne. ( akoi hanyar da tahadasu dama).

2- Anasamun ciwon kunne ta dalilin shigan wani Abu kamar Burbushin Kura, Gashin magye da sauransu ( Allergies).


HALAMUN CIWON TSAKIYAR KUNNE :  

1- Mutun zaiji kamar wani abu ya cika masa kunne .
2- Rashin ji sosai
3- Zubar da ruwa a kunne
4- Jin zafi a cikin kunne .
5- kaikayin
6- Zazzabi da ciwon kai .


MENENE ALAKAR MURA DA CIWON KUNNE :  

Gaskiya akoi alaka tsakanin mura da ciwon kunne, mafi yawan mura yana kama hanci da makogoro kuma idan Baku manta ba munce akoi hanyar da tahada tsakanin Makogoro da Hanci dakuma tsakiyar kunne.  Kamar yadda mukace kwayoyin cutar bakteriya, da virus da kuma burbushin kura su suke kawo ciwon kunne. To wadannan kwayoyin cutar su suke kawo Mura kuma suna samun hanyar shiga kunne ta wannan hanyar da tahada tsakanin makoro, hanci da kunne.


SHIN DIGAWA KUNNEN MAN ZAITUN YANA MAGANI CIWON KUNNE :  

Kuskure ne digawa kunne man zaitun, bama man zaitun ba ko maganin ciwon kunne irin su gentamycin bai kamata a digawa kunne ba, in bada izinin likita ba.  Dalili shine wani lokocin ana samun fujewan dodon kunne (rupture of earwax) lokocin da ake ciwon kunne to ko wanne  irin abu idan yawuce can ciki zai iya kawo matsala.


MAGANIN CIWON KUNNE :  

Tabbas duk wani ciwon kunne da kwayoyin cutar bakteriya takawosu ana amfanida ANTIBIOTICS wajen treatment , hakanan wanda aka samu da dalilin Burbushin kura ana amfani da ANTIHISTAMINES.



ABUN LURA DA HANYOYIN KARIYA:

1- Kada a wanke kunnen yaro wai dan sabida yana ruwa. Bincike ya nuna akoi sinadarai guda goma a tsakiyar kunne wanda aikinsu shine hana shigar kwayoyin cuta, tham a garin wanke dauda idan aka wane wadannan sinadaran shikenan anbudewa kwayar cuta kofa.

1- Gangar tsakiyar kunne musamman na yara batada kwari a garin wankewa zai iya fashewa wanda hakan zai iya kawo rashin ji kwatakwata.

2- Shayar da yara da nonon uwa zalla ba tareda an garwaye shi da ruwa ko Abinci.  Kuma kada abawa yaro nono a kwance sabida yakan iya kawo ciwon kunne.

3- Kada ayi amfani da tsinke ko fiffigen tsunstu wajen tsosawa yaro kunne ko babba domin tana kawo rauni ga gangan tsakiyar kunne.

4- kada a jiye yaro kusada inda hayakin taban sigari yana tashi domin shima yakan taimaka wajen kawo wannan matsalar. 

5- Yiwa yaro allurar rigakafi da yana rage wannan matsalar, musamman allurar rigakafi irinsu na kyeda da Kuma na mura Mai kama hanyar numfashi.

6- Ba'a digawa yaro maganin ciwon kunne a kunne ko wacce eri saida amincewar likita. 






Lafiya Uwar Jiki, Babu Mai Fushi Dake!

....Lalle wannan magana haka take, domin a 'yan kwanakin nan an binciki file dina (nayi rashin lafiya) Wanda hakan yasani na qara fahimtar ba arzikin da yakai na lafiya a duk  fadin duniyar nan. Wato ciwon nan daya rafkeni.....(abin sai dai shukran).
Hakan nema yasani yin wannan rubutun domin na tunatar abisa ga dogaro da wannan ayar: “And Keep Reminding because reminding Benefits the believers." (5:155)

Ya Kai dan-uwa a duk sa'dda da Allah (s) ya wayi gari ka tashi ka jika lafiyarka qalau to 
Ka good masa bisa ga wannan babbar baiwa da ni'ima da yayi maka!

Da haka nake cewa, Allah ka qara mana lafiya da Arziqi mai albarka. Marasa lafiya da suke a gida da asbiti suma ubangiji Allah ka sauwaqe musu!


Uhm! A wancan lokacin da nake kwance, abincima ina son naci amma bazai ciwuba sakamakon bakina ya Zama testless. Ko tuwo aka kawo inaji ina kallo Saidai.....

 Amma Yanzu Alhamdulillah! Lafiya ta samu, ga masu niyyar kawo mini lemo da kaza to kofa a bude take! Hahhhh!

Eh Baza mu manta da irin dawainiyar da su Sufi suka Shiga ba, Allah ya saka da alheri!

Signed:
thë2ßrøthêrs

'Yar Wuya/Beli

CIRE YAR WUYA DA KUMA BELI A JARIRAI. 

....Abisa duba ga wasu daga cikin al'adunmu na Hausawa, Hakan yasani wasu 'yan nazarce- nazarce wanda har a qarshe ya kaini ga yin rubutu Akan maudu'in dake a sama, tare kuma da Kokarin samo amsoshin wasu tambayoyi da nayi kamar haha:

 Shin hakan yana da wani fa’ida a likitance? Duba da irin yanda yaran ke shan wahala bayan cire mu su. Me yasa ake cirewa? Sannan me zai faru idan ba’a cire ba?! 

A mahanga ta likitanci cire wadannan abubuwan ba shi da wani fa’ida (medical benefit), sai dai ma ayi batun illa. Sannan duk dalilan da aka kawo na cirewar (ga masu cirewa kenan) idan mutum ya yi nazari, zai ga cewa ba su bayar da wata ma’ana ba.

A addinance kam akwai ‘controversies’ da yawa akan abun. Wasu Malaman sun tafi akan cewa wajibi ne a cire, wasu kuma sun ce yana da kyau a cire (amma ba wajibi ba), wasu kuma sun dauki matsayar cewa kar a cire.


A zahiri dai, ya fi kama da al’ada kawai, wacce ta fi shahara a kasar Hausa. Kuma kamar yanda muka sani, akwai al’adu da yawa wadanda suke cutarwa (Harmful Traditional Practice) ga lafiyar mutum, amma ana yin su. Cire ‘yar wuya da kuma beli sun fado cikin misalan wadannan al’adun; wankan jego da tafasasshen ruwa, shan kunun kanwa wanda ya wuce qa’ida ga mata masu juna biyu/ masu shayarwa, yin shayi/kaciya ga mata, dss; na kadan daga cikin wadannan al’adun.



- MENENE BELI? 

Shi ‘Beli’ sunan shi “Uvula” a likitance. Shi ne ya rufe tsakanin baki da makogoro.. (Da yake likitanci ba da Hausa ake koyar da shi ba, wasu lokutan sunayen kan iya canjawa ‘depending’ on yankin da mutum ya ke).

Babu wani ‘Medical benefit’ na cire shi a jikin jariri gaskiya. Wadanda suke cirewa sun yi ‘theorizing’ cewa yana hana gudawa da amai (amma ba su yi bayanin ya hakan ke faruwa ba), yana kawo shakewa idan ana shayar da jariri, sannan kuma wai saboda tsoron kar ya kumbura idan cuta ta kama shi.

Amma kuma illar cire shi ya fi yawa. Kama daga ballewar jini, da kuma kassara ‘normal anatomical presentation’ na bakin mutum, yiwuwar wucewar abu daga bakin mutum zuwa cikin hancin shi, da kuma daga baki zuwa huhu idan jariri, dss.

Babu wani dalili da zai sanya a cire ma jariri Beli matukar ba wai yanayi ya bada hakan ba ne, kamar misali kamuwa da wata cuta, dss.




- MENENE 'YAR WUYA? 

Kamar yanda nace Hausa na bambanta. Wasu na kiran shi hakin wuya, wasu kuma ‘yar uwa. Kila a wani wajen ana kiran shi wani abu ne ma daban.

Shi kuma ‘yar wuya shi ne “Palatine tonsil” [wannan shi aka fi cirewa, kuma shi ya fi hadari]. Saboda ko ba komai su “tonsils” generally kamar misalin barikin sojoji ne a kasa, inda ya ke tattara sojoji ya basu horo. A cikin ‘tonsils’ ne ake samun ‘immune cells’ [wadanda kamar su ne sojojin jikin mutum da ke yaqi da cututtuka] da ke kare jiki daga kamuwa da wasu kwayoyin cututtuka. Ka ga idan aka cire shi (tonsil) daga jikin mutum, zai zama kamar an cire sojoji daga kasa ne a lokacin yaqi ko?

Duk wata kwayar cuta da ta shiga bakin mutum kafin ta je makogoro, sai wadannan “Palatine tonsils” din [su ne kuma ake ce ma ‘yar uwa] sun tare ta, sun yaqe ta domin su hana ta wucewa. Idan babu kai tsaye zata wuce zuwa makogoro kenan; daga nan kuma sai inda Allah Ya yi. Akwai shi kan shi makogoro, akwai ciki, akwai hanji, akwai hanta, akwai huhu; duk cuta zata iya zuwa musu daga baki.

Binciken likitoci ya tabbatar da cewa, jariran da ake cire ma ‘yar wuya din nan sun fi kamuwa da cututtuka fiye da wadanda ba’a cire musu ba. Musamman cututtukan da suka danganci baki, hanci da kuma makogoro.

Akwai yanayin da zai iya bayar da cewa a cire din, misali idan suka kamu da cuta suka kumbura da kuma barazanar yada cutar zuwa wani sashe daban na jikin mutum. Ana cirewa, ba su kadai ba ma; har sauran “tonsils” ana iya cirewa idan yanayin cuta ya bada. Amma idan babu wani dalili, sam bai kamata ake cirewa jarirai ba.




A takaice dai ba shi da wani fa’ida a likitance cire wadannan abubuwan. Kowanne daga cikin su yana da amfani a jikin jariri. Jikin dan Adam shi ne cikamakon halitta, duk abun da ka ga Allah (T) Ya halitta a jikin dan Adam, akwai amfanin shi. 

Allahu a’alam..


          >>>>> Yours Dom-Domty <<<<<


....Ku Kasance da shafin Dom-Domty a Koda yaushe, domin samun bayanai da fadakarwa da suka shafi harkar kiwon lafiya!




   Sannan Angaida Yara Manyan Gobe!




Signed:
thë2ßrøthêrs

Sunday, January 26, 2020

FADAKARWA:

LASSA FEVER


Lassa fever ( haemorrhagic fever) : cuta ce da akan dauketa ta hanyar idan abinci ko abin sha ta gurbata da fitsari ko kashin bera irin ta jeji, kwayar cutar Lassa Virus ce take kawo shi.

Sauran hanyoyin kamuwa da cutar sun hada da cudanya da wanda ke dauke da cutar.

Haka kuma jami'a da mai dauke da cutar na iya jawo wannan cutar ta Lassa fever.

Bayan mutum ya kamu da cutar alamomin cutar kan fara bayyana daga kwanaki biyu zuwa mako uku.


ALAMOMIN LASSA FEVER

Kamar yadda babbar hukumar lafiya ta Duniya (WHo) tafitar alamun kamuwa da cutar sun hada:

1- Zazzabi mai zafin
2- Amai
3- Gudawa mai jini
4- Fidda jini ta kafofin jiki.


HANYOYIN KARIYA :

1- Kada ayi amfani da abinci wanda za'aci ba tareda sai an wanke ba kamar su garin kwake.

2- Duk matar da ba'a yarda da tsaftar ta ba a kauracewa abincin ta .

3- A kiyaye tsabtar muhalli da abinci da ake amfani da ita .

4- A rufe duk wani abinci da abin sha da aka ci aka rage kuma a dumama shi kafin asake amfani.

5- Kada aci kayan Lambu  Irin su salat wanda ba dafasu akeyi ba ,sai an wanke da ruwan manda .

6- Wadanda wannan cutar ta kamasu a kyebesu da haduwa da wassu jama'a.

7- A tabbatar an tace sannan a tafasa ruwan da aka debo daga rafi ko rijiya kafin a sha .

8- A tabbata an wanke hannaye da sabulu kafin cin abinci da bayan cin abinci.

9- Wandan da suka kamu da wannan cutar kuma suka warke a hakura da jima'i na tsawanni sati 2 zuwa wata Daya.

10- Idan akaga wadannan alamomin ayi gaggawa akai mara lafiya zuwa asibity.

11- Anemi shawarwarin likitofi kafin ayiwa gawa wanka wanda yamutu da wadannan alamomin.




PUBLIC ANNOUNCEMENT.  

Take/report any person with the following symptoms to the nearest health facility/hospital: 

1. High grade fever
2. Bleeding from especially nose and ears
3. General body weakness/muscle pain
4. Malaise
5. Headache
6. Sore throat  Ensure personal and environmental hygiene.


Haemorrhagic fevers (e.g. Lassa fever and Ebola fever) are real. 


May God save us all.

Signed: 
thë2ßrøthêrs