Responsive Ads Here

Saturday, April 27, 2019

Read And Think About It.

              BARKANKU DA WARHAKA!



           Darajar Mutum Da Cikar Kimarsa:

Babu Wani Yanayi Dayake Tabbacec-ce ne A Rayuwar Duniyan nan.

Domin kuwa duk tsayinka, Baka isa ka hango gobeba. (Sabida haka, ka zamto mai hakuri).

Sannan komin girmanka da Kuma karfinka, Bazaka iya daukan kanka zuwa kabarinka ba. (Sabida haka, ka zamto mai tawali'u).


Haka nan duk komin yawan arzikinka na dukiya da kuma wadata da kake dashi, Bazaka Sanya hula guda goma a kanka ba, ko Sanya takalma guda goma kala daban a kafarka ba. (Sabida haka, ka dauki rayuwa a matsayin abace mai Sauki).


✓.  Kada ka damu da abin da ya wuce, don ba zai dawo ba. 

✓.  Kada yau ta sha ma kai, domin gobe ma rana ce.

✓.  Ka zamto mai Yafewa wanda ya cuce ka, domin ni'ima ce. 

✓.  Kar ka zamto mai yawan tuna abin bakin ciki da damuwa, domin wahala ce. 

✓.  Kar ka zamto mai Manta Alheri, domin yin hakan Butulci ne.

✓.  Kafin ka roki Allah abinda ba kadashi, ka fara gode masa akan abinda kake dashi, don shine ya baka.

 ✓.  Muddin kana Raye, ka zamto mai daukan darasi, domin Rayuwa Haske ne, Mutuwa kuwa Aya ce.


                    ...just comment with:
                          الحمدلله، ماشاءالله


If you think it is your alarm clock that wake you up every morning, then try putting it beside a dead body and you will realise that it is the grace of God that woke you up every day.





     ....Kai! azumin Yau Akwai Wahala! !!

the2brothers

0 comments:

Post a Comment