Responsive Ads Here

Saturday, March 9, 2019

Ciwon Diabetes

MENENE DIABETES?



Diabetes: 

Diabetes wata cutace da ake kiranta cutan suga da Hausa, cutace wadda suga (glucose) dake cikin jini yake haurawa sama.



MENENE DIABETES TYPE 1:



Diabetes type 1: 

Diabetes type 1 (Insulin Dependent Diabetes): Idan suga yayi yawa a jikin dan Adam Dalilin Jikin mutun baya Samar da kemikal mai suna Insulin shi ake kira Diabetes Type 1.

MENENE DIABETES TYPE 2 :



Diabetes type 2: 

Diabetes type 2: Idan suga yayi yawa a jikin mutum a dalilin rashin samun isheshahen Insulin shi ake kira Diabetes type 2.


SHIN YARA ZASU IYA KAMUWA DA DIABETES?


Eh, Yara suna kamuwa da diabetes, diabetes type 1 yafi kama yara fiyeda manya shi yasa ake kiransa juvenile diabetes.






SHIN MAI DAUKE DA DIABETES ZAI IYA RAYUWA KAMAR SAURAN MUTANE?

Eh zai iya rayuwa yadda wasu suke rayuwa ko yana dauke da ciwon suga amma da sharadin zai kiyaye da dokoki da likitoci suka daurashi akai.



WADANNE ALAMUNE AKE GANE CUTAR DIABETES DASU?

Yawan Jin Yinwa.

Yawan Jin Ishirwa.

Yawan Yin Fitsari.


Ramewa Mara Dalilin.

Bushewar Fata.

Gani Dishi Dishi.

Mutun Yaji Kafarsa Kamar Baya Jikinsa.

Kaikayin Jiki.

Dadewar ciwo ba tareda warkewa ba.

Yawan Samun sanyin gaba (Vaginal infection)


Daga Karshe Muna Bada Shawara Wanda yake fama da wadannan alamomi yakamata yaje asibity domin adubashi kuma asan yawan suga nashi.





via: Dom-Domty Medical Tips



مصطفى عبدالمؤمن-
the2brothers



0 comments:

Post a Comment