AMFANIN AZUMI GA LAFIYA!
Azumi, kamar yanda muka saba, shi ne kamewa daga cin abinci ko shan wani abu har zuwa wani lokaci. Wannan ‘literal definition’ kenan. Wasu na yin Azumi bisa al’ada ne, yayin da wasu kuma ke yin shi a matsayin Ibada; sai dai kuma bai tsaya iya nan ba kawai, domin yana da matukar amfani ga lafiyar dan Adam.
An raba azumi zuwa kala biyu ne a lafiyance. Na farko ‘Intermittent fasting’ shi ne irin wanda muka sani, mutum ya kame daga ci da sha na tsawon wasu awanni a rana, daga baya kuma ya dawo ya ci abinci a sauran awanni. Na biyu kuma, ‘alternate fasting’ shi ne mutum ya dauke tsawon rana din baki daya bai ci komai ba, bai sha komai ba; watarana kuma sai yaci abinci, ba tare da yin azumi ba. Kowanne daga cikin wadannan kalar azumi na da amfani ga lafiyar dan Adam. Sai dai kashi na farko, ‘Intermittent’ ya fi. Ko ba komai ya fi kashi na biyu ‘complications’. Kuma shi kashi na biyu idan ba wai bisa kulawar masana lafiya ba, yana iya komawa abun da ake ce ma ‘starvation’ (cutar yunwa), wanda zai iya illata mutum sosan gaske.
Bisa halitta jikin dan Adam na daukan akalla awanni 24 ne (kwana guda) wajen sarrafa abincin da mutum ya ci. Wato, har zuwa tsawon awa 24 din nan jikin mutum zai iya ‘adjusting’ kan shi ta hanyar wasu matakai (processes) domin samar da abincin da ‘cells’ za su yi amfani da shi wajen gabatar da ayyuka. Ashe kenan cewa,
duk wanda ya yi ‘Intermittent fasting’ har lokacin da zai sha ruwa akwai sauran wani ma’adanin abinci a jikin shi, wanda ba
lallai an yi amfani da shi ba ma. Wannan rahamar ce ta sanya mutane ke iya Azumi daga kwanaki har zuwa tsawon watanni, ba tare da sun illata ba.
Kamar yanda yake Allah (T) ne kadai Ya bar ma kan Shi sanin irin dimbin ladan da Azumi yake da shi, haka zalika, Shi kadai Ya san irin dimbin amfani da yake da shi ga lafiyar dan Adam. Wasu kadan daga ciki su ne:
1. Rage Kiba:
Kiba (Obesity) cuta ce mai hadarin gaske. Wacce take iya haifar da muggan cututtuka kamar su Hawan jini, Ciwon zuciya, ciwon
suga da sauran su. Yin azumi yana rage yawan kibar mutum sosai, ta hanya mafi sauki. Akwai binciken da ya nuna cewa, baya ga motsa jiki (exercise) babu abun da ya kai yin Azumi rage kibar mutum. Ta hanyar rage kitse ‘fat’ da Azumi ke yi, zai taimaka wajen rage yiwuwar kamuwar wadancan muggan cututtuka, ma su kashe mutum lokaci daya.
2. Kariya daga cutar kwakwalwa, da kuma ciwon daji (Cancer):
Bincike ya tabbatar da cewa yin Azumi yana rage yiwuwar kamuwa da cututtukan kwakwalwa marassa magani (Neuro-degenerative diseases) da kuma ciwon daji (cancer) ta wata hanya da ake ce ma
‘Autophagy’ (cinye kai). Akwai wasu sinadarai da ke cinye duk wani ‘protein’ da ya gama aiki ko yake da matsala a jikin mutum, Azumi na sanya kara yawan wadannan sinadaran a jikin mutum. Ta
haka, duk wasu ‘proteins’ da suka gama aiki za’a gama da su, a fitar da su daga jiki baki daya. Wannan ba karamin rahama ba ne ga al’umma.
3. Kara Lafiyar Ciki da Hanji:
Ta hanyar rage cin duk wani abu da ya zo hannun mutum, kamar yanda aka saba idan ba’a Azumi; ciki da kuma hanji na samun isashshen lokacin da za su gama da dukkan abun da yake cikin su yanda ya kamata. Sabanin idan ba’a azumi yanda kila duk kusan bayan awa daya sai mutum ya jefa wani abun cikin shi (wani abun ma bai dace a ci ba).
4. Karin Girma, da kuma Rage Kumburi:
Bincike ya tabbatar da cewa, Azumi na sanya a saki sinadarin karin girma a jikin mutum (Growth Hormone secretion). Wanda baya ga karin girma, har wala yau, yana taimakawa wajen sarrafa wasu muhimman ayyuka da jikin mutum (metabolism), wanda ta hanyar shi ne ake ‘controlling’ duk wani aiki na jiki. Kari akan haka, shi ma yana taimakawa wajen rage kiba.
Rage kumburi (inflammation), yana taimakawa wajen rage yiwuwar kamuwa da cututtuka irin su ciwon daji (Cancer) dss.
5. Rage yiwuwar kamuwa da cututtuka kamar su Ciwon Suga, Hawan jini..
Azumi, ta hanyar rage kitse (body fat) daga jikin mutum, yana taimakawa wajen kariya daga cututtukan da suka fi yawan kashe
mutane a duniya yanzu. Ciwon zuciya (Myocardial infarction) shine abu na biyu da ya fi kashe mutane. Ciwon Suga (DM) ya zama ruwan dare, kuma daya daga cikin cutar fa tafi kowacce yawan kashe mutane. Hawan jini, wanda ya zama kamar abun yayi; na daya daga cikin mafi munin cutuka da ke kashe mutum ‘silently’.
6. Tsawon Rai:
Idan aka hada ‘process of autophagy’ wanda ake cinye ‘proteins’ din da suka gama aiki ko suka samu matsala; da kuma irin kariya daga wasu mugayen cututtuka da suka fi kowanne kashe mutane, za mu ga cewa, Azumi ba wai kawai yana kara lafiya ba ne, yana kara nisan kwanan mutum ne kai tsaye. Bincike ya tabbatar da cewa wadanda ke Azumi sun fi wadanda ba su Azumi jimawa a duniya. Sun fi su rashin tsufa da wuri, kuma sun fi su rashin mutuwa da wuri.
DOM-DOMTY ®
Via: Dom-Domty Medical Tips
....Munayi Muku Fatan Alkairi!
(Dafatan 'Yan-uwa Da Abokai, Bazaku Mance damu Acikin Addu'o'inku da kuke gabatarwa Acikin Wannan wata mai Alfarma ta Ramadan ba!) Ma'assalam.
Ayi Buda Baki/Sha Ruwa Lafiya.
محمد مصطفى
the2brothers

Shukran Lakum, Jazakumullahu bi Khairin!
ReplyDelete