CIWON BASIR (PILES)
Ciwon basir ciwo ne da ke haddasa kumburi da radadi mai tsanani a duburan mutum (lowest part of rectum and the anus). Ciwon kan haddasa rashin jin dadi a wurin da kuma zubar da jini wani lokacin.
Ciwon Basir Ya kasu kashi Biyu ne;
1- Akwai na waje (external hemorrhoid)
da kuma,
2- Na ciki (internal hemorrhoid).
Ga bayaninsu kamar haka:
Ciwon Basir Na Cikin Dubura (internal hemorrhoid):
Kamar yadda aka kira shi, wannan ciwon basir na daga cikin duburar mutum (inside rectum) ne. Mutum ba ya iya taba shi da hannun saboda ya na boye ne ta ciki. Yawanci irin wannan basir din bai da zafi, saboda a wurin da ya ke, wato rectum. Abinda ke sa mutum ya ji zafi kadan ne, wato yana da pain-sensing nerves yan kadan. A kan gane mutum na dauke da irin wannan basir ne in ya na zubar da jini, wato yana bleeding, a Turance.
Ciwon Basir Na Wajen Dubura (external hemorrhoid):
Ciwon basir na wajen dubura dai shine wadda ke fitowa a kan fata ta wajajen dubura (anus). Shi wannan irin ciwon basir ya na da zafi ko in ce radadin gaske saboda wurin na da abinda ke haddasa radadi da wuri (pain-sensing nerves). Wani dan kunburi kan samu a wurin wadda kan kunshi jini (blood clot), sannan wannan kunburin akasari kalarsa kore ne, wato blue ko kuma purple. Ya kan haddasa zafi mai tsanani da kaikayi harma ya kan yi jini wani lokacin. Ko da kumburin ya sabe mutum kan saura da shi kadan, wadda ke haddasa dan rashin jindadi a wurin wani lokaci.
Abubuwan da Mutum zaiyi Don Gujewa kamuwa da Ciwon Basir:
๐ Mutum kan iya rage hatsarin kamuwa da basir ta hanyar kula da yadda ya ke tafiyar da rayuwan shi ta inda ba zai samu matsalar bahaya mai karfi ba, wato constipation. Kuma mutum zai iya cimma hakan ta hanyoyi kamar haka:
๐ Yawan shan abu mai ruwa-ruwa: A kalla mutum ya kasance yana shan ruwa kamar kofi 8 zuwa 10 a ko wacce rana. Sannan ya samu a kalla lemun ‘ya’yan itace (fruit juice) kamar kofi biyu kullum.
๐ Cin abinci mai high fiber: Abinci kamar su danyun ‘ya’yan itace, ganyayyaki (vegetables), irin su bran cereal da sauran abinci masu dauke da fiber a ciki.
๐ Yawan motsa jiki: motsa jiki kamar irin walk da aerobics dinnan su na da kyau ga lafiya. Amma ya na da kyau mutum ya nemi shawaran kwararru kafi fara yin exercise.
๐ Yana da matukar muhimmanci mutum ya kasance ya na zagawa akai-akai (bowel movement) da ya ji bukatan hakan saboda jinkirtawa kan haifar da constipation.
๐ A kiyaye hada kiba: Mutum ya kamata ya yi kokarin tsayawa a adadin nauyinsa kamar yadda kwararru suka tabbatar masa. Hada kiba ya yi yawa kan sa wa jiki nauyi wadda hakan na haddasa ciwon basir.
๐ Yana da kyau a rika yin gwajin nauyi lokaci-lokaci don gudun wuce gona da iri.
๐ A rage yawan tsayuwa ko zama mai tsayi: In har mutum ya kasance sai ya zauna zama mai tsayi soboda sana’arsa ko dalilai makamantar wannan, to ya na da kyau ya rika tashi duk bayan awa daya haka, ya dan gewaya kadan.
Wasu Abubuwa ne ke Haddasa Ciwon Basir?
Masana sun yi ittifaki abubuwan dake jawo ciwon basir sun hada da:
1. Gado (genetics):
Mutane kan kamu da ciwon basir ne wani lokaci saboda gado da sukan yi a wajen iyayensu ko kuma danginsu.
2. Kiba (obesity):
Saboda nama da masu kiba kan hada a kasan su (lower rectum), tafiyan jinin su, wato blood flow, kan samu matsala. Hakan sai ya sa jijiyoyin wurin su kumbura wadda hakan kan zama ciwon basir.
3. Juna Biyu (pregnancy):
Mata da yawa kan samu ciwon basir a yayin da suke da ciki, musamman lokacin da mace ta kai irin wata bakwai ko sama da haka. Wannan basir na faruwa ne saboda da irin yadda wasu matan kan fuskanci wuyan bahaya, abinda ake kira constipation a Turance, dalilin irin matsuwa (strain) da wurin ke samu a dalilin nauyi da suka kara ko makamancin hakan. Wani lokaci kuma nauyin yaro ne kan yi wa uwa yawa sai ya sa jijiyoyin ta na kasa su matsu, to shima wannan yanayi kan haifar da ciwon basir ga mace mai juna biyu.
4. Straining (wato matsuwa):
Matsuwa ba dole sai mace na da juna biyu ba ya ke faruwa. Yakan faru saboda wasu dalilai daban. Idan kuna hakan ya faru, yakan jawo ciwon basir saboda matsuwa da jijiyoyin kasan mutum (rectum) kan yi, kuma yakan haifar da kumburi ko kara fadin wurin. A wani lokaci ciwon kan fito waje ya dan yi kumburi haka mai dan laushi sannan ya rika zafi a yayin bahaya. Amma yawanci wannan kumburin kan koma don kansa ko kuma in mutum na iya mai da shi a hankali.
5. Gudawa Mai Tsawo:
Ciwon basir na wanzuwa idan mutum ya na gudawa mai tsawo, wato ya kasance mutum ya dauki lokaci mai tsawo yana bahaya kuma gudawa. Har’ila yau yakan wanzu dalilin irin bahayan nan dake fita da kyar, wato constipation. In mutum na tari abun kan kara tsananta.
Baya Ga Wadannan Dalilai da Muka Ambata A Baya, Har’ila Yau Mutum Na iya Kamuwa da Ciwon Basir ta:
Hanyar daga kaya mai nauyi
Yawan tsayuwa mai tsayi ko kuma zama mai tsayi.
Tsufa
Lokacin daya kamata Aga Likita:
A yayin da aka gwada duk abubuwan da muka ambato a saman nan amma ba ga alamun sauki ba, ko kuma anga jini na zuba, to lallai ya kamata a ga likita cikin gaggawa don samun kulawar kwararru. Allah ya sa mu dace.
Maganin Ciwon Basir:
๐ Abin murna anan shine yawa-yawancin lokaci ciwon basir na warkewa da kansa.
๐ Amma ga wasu hanyoyi da mutum zai bi a samu sauki daga radadin ko kunburin ko kuma kaikayin ciwon basir:
๐ Zama cikin ruwan dumi (ba ruwa mai zafi ba) na kamar minti 20. A yi haka sau da yawa a rana.
๐ A tambaya likitoci irin mai, wato cream da ya kamata a yi amfani da shi, a kwai su da yawa a kasuwa.
๐ A yi amfani da toilet paper mara damshi don goge wurin. Wasu kanyi amfani da tawul mai damshi ko toilet paper mai damshi zasu taimaka.
๐ Wurin ya kasance cikin tsafta a koda yaushe. Amma yin amfani da sabulu kan iya kara ingiza ciwon. Sai a kula.
๐ A tabbatar an goge wurin a hankali bayan wanka. Barin wurin da damshi kan iya sa kaikayi.
๐ A dannan wurin da kankara na minti 10 kamar sau hudu a rana.
In har basir din ya fara fitowa, to yana da kyau a maida shi a hankali.
๐ Amma a tabbatar hanu na da tsafta kafin a yi hakan.
....A Karshe Munayiwa Masu Fama da Wannan Ciwo Na Basir Fatan Allah Ya Sauwake Ya Kuma Basu Lafiya!