Responsive Ads Here

Wednesday, March 29, 2023

Dom-Domty Branch

          Alhamdulillah masha Allah! 



Muna qara yiwa Allah godiya daya kawo mu wannan lokaci, wanda gashi daya daga cikin Yaran Shagon Dom-Domty mai suna Hassan Musa ya samu qaruwa na bude sabon shago acikin kasuwar Gombe.



Muna farin ciki tare kuma da addu'ar Allah ya Sanya albarka aciki. 

Allah ya Sakawa me gidanmu Alh. Malam Abdullahi Hassan Dom-Domty da alkairi. Muna rokon kuma Allah ya qara masa lafiya da yalwar arziki. Wanda wannan dama ba shine karo na farko ba, akwai sauran yaran shago da Dom-Domty ta yaye kamar su:

Adamu Muhammad Hassan (kyali)

Abbakar Usman Hassan (small)

Wanda suma duk sunada shago yanzu acikin kasuwar, sai kuma Muhammad Sageer Yayari da kuma Mustapha Abdulmumini da Hassan Musa.



A karshe muna mika gaisuwa ga babban mai gida wato Alh. Adamu Hassan Bamatsala, da kuma karamin mai gida Alh. Salisu Hassan.

Muna fatan Allah ya qaro lafiya da kuma yalwar arziki mai albarka.



Sunday, March 26, 2023

Ramadan Kareem

 Alhamdulillah Masha Allah!

Barka da Shan Ruwa/Buda Baki 


Dom-Domty Medicine Store: keyi muku barka da warhaka da fatan ansha ruwa lafiya, tare kuma da addu'ar Allah ya karba mana ibadunmu.

Muna rokon Allah ya samu acikin 'yantattun bayinsa daya gafartawa acikin wannan wata mai alfarma na Ramadan.   

Har wala yau Dom-Domty na marhaban ga dukkanin customers nata da kuma masu sayen daya ko sari zasu samu Ramadan Discount insha Allah.


...Come Ones, Come all 

You are welcome!

Saqo daga: Abbakary P.A Bamatsala 


Tuesday, January 24, 2023

Breaking News

 ....from Dom-Domty.


We here by wish to inform our esteemed customers  that Dom-Domty Medicine Store will stop collecting old Naira notes for any transaction as from today 11:59pm.


Dom-Domty Medicine Store na sanarda kostomominta cewa, zata daina karban tsofaffin Kudi daga gobe laraba 11:59 pm.

A sabida haka muna masu baku hakuri kan dukkan wani takura da zaku iya fuskanta a dalilin haka.

Sa Hannu: Abbakary P.A Batsala.


               ☆via-the2brothers-links☆

Sunday, January 1, 2023

New Year Message

 ....time is going, Now it's 

             Dom-Domty @2023.

Sakon Taya Murna da kuma Jaje daga Dom-Domty.


Alhamdulillah may Allah sub-hanahu wa ta'ala make this year better than the previous one.


A zahirin gaskiya kwanakinmu suna raguwane a yayinda shekarunmu kuma yake qaruwa. To saisa ya zamto murna da jaje.

Allah ya Kara aramana dama dazamu sake kusantarshi  domin yamana gata daya sake samu cikin Wanda zamu ga sabuwar shekara  

Daga karshe muna fatan Allah ya sa munshigo a sa'a. Muna rokon Allah ya hadamu da alkairin dake cikin wannan shekaran  Kuma muna rokon Allah ya karemu da sharrin dake cikinsa Allah yadatardamu alkairi yasa yanda muka ga farkonsa lafiya yasa muga karshensa lafiya.


Muna yiwa kowa fatan alheri, Bissalam.




Tuesday, October 11, 2022

Happy Maulud-Nabiy (s)


 Bismillahir-Rahmanir-Rahim!

Godiya ya tabbata ga Allah ubangijin talikai.

Tsira da Aminci su qara tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad (s.a.w.a).

Muna farin cikin taya al'ummar musulmin duniya murnar ranar haihiwar Annabi (s) na shekarar 1444/2022.


Muna fatan Allah ya mai-maita mana, ya qara mana soyayyar Annabi (s) da iyalan gidansa tsarkaka.



Saqo daga P.A Bamatsala da sauran yaran shago.
Via: Dom-Domty 




Angaida Mustapha Garkuwa 

Thursday, October 7, 2021

....Such is Life!

via-the2brothers-links

Masha Allah! Shukran lillah!



Happiness is always a choice. You can't wait for circumstances to get better. You have to create your own good fortune. So look for ways to be happy every day. You learn more from failure than successDon't let it stop you. failure builds character.



Akramakallahu Malam Auwal Sufy da almajiransa.😜



Yallaboi Abbakary P.A Bamatsala.


Hassan Musa.


Muhammad Garba (baba).

Abubakar Usman Hassan.


Mustapha Abdullahi (Jimne kilefa).

Mustapha Mahmoud Adam (Garkuwa).

Auwal Abubakar (Boxy).

Akramakallahu Manyan Sufaye😉

Abubakar Hassan Brown (Dakare). 

Alh. Salisu Hassan (Khausar Med. Store).

Auwal Muhammad Maigari.

Hashimu Musa (kwaro).

Yallaboi Masu Jimnekilefa.

Ammar Abubakar (Madugu).

....Sannan muna mika gaisuwarmu ga sauran 'yan-uwa da abokai wadanda bamu samu damar sako hotonsu/ambatarsu ba, Allah yabar xumunci.🙏

Don't always be a worried person, but most time, be a concerned person. Because a worried person sees a problem, but a concerned person solves a problem. Remember, the finger that wipe your tears during a hard times is greater than thousands hands that clapped for your success. Always look back and see where you are coming from.

God protects us!



Tuesday, September 7, 2021

Kwarangwal (skeleton)

Abubuwan Ban Mamaki 15 Gameda Kwarangwal:


 Kwarangwal shine jerin kasusuwan jiki kuma ginshikin dake rataye da dukkan sassan jiki.



1. Akwai ƙasusuwa daban-daban har guda 206 a jikin mutum. 

2. Jarirai sun fi manya yawan ƙasusuwa, a yayin da manya ke da ƙasusuwa guda 206,  jarirai na da ƙasusuwa kusan 270, inda yawansu zai ɗinga raguwa yayin girmansu saboda haɗewar wasu daga cikin ƙasusuwan har su zama dai-dai da na manya.

3. Fiye da rabin ƙasusuwan ƙwarangwal — ƙasusuwa 106, suna nan a tattare a hannaye, tsintsiyoyin hannu, da kuma tafukan sawu.

4. A tafin sawu ɗaya kawai, akwai ƙasusuwar har guda 26.

5. Hannu haɗi da tsintsiyar hannu na ɗauke da ƙasusuwa har guda 27.


6. Ƙashin cinya shi ne ƙashi mafi tsayi kuma mafi ƙwari a jikin mutum.

7. Ƙashi mafi ƙanƙanta kuma mafi ƙarancin nauyi shi ne ƙashin 'stapes' da ke tsakiyar cikin kunne, ɗaya ne daga cikin ƙasusuwa uku da ke tsakiyar cikin kunne da ke temaka wa wajen sarrafa sauti.

8. Ƙasusuwa na gama tsayin ne bayan balaga zuwa wajejen shekara 25, amma kauri, nauyi da ƙwarin ƙashi za su ci gaba da caccanzawa tsawon rayuwa.

9. Ƙashin 'hyoid' shi ne ƙashi ɗaya tak da bai jingina da wani ƙashi ba. Wannan ƙashi mai sifar "V" na nan tsakanin maƙogaro da tushen harshe.

10. Muhimman sinadaran ginin ƙashi sun haɗa da kalsiyam (calcium), fasfaras (phosphorus), sodiyam (sodium) da sauransu. Don haka cin abincin da ke ɗauke da waɗannan sinadarai na temakawa wajen gina ƙashi.

11. Kamar yadda ƙwarangwal ya zama ginshikin jiki, haka nan tsokokin jiki sune ke samar da ƙarfi / yunƙurin da ke motsa sassa ko gaɓɓan jiki.

12. Ƙwarangwal na samar da kariya ga muhimman sassan jiki kamar ƙwaƙwalwa da ke ƙunshe cikin ƙoƙon kai, laka da ke ƙunshe cikin kwaroron ƙashin gadon baya, ƙwayar ido da ke cikin gurbin ido da kuma zuciya da huhu da ke cikin kejin haƙarƙari.

13. Dogayen ƙasusuwan ƙwarangwal da ke ƙunshe da ɓargo a cikinsu na daga cikin sassan jiki da ke samar da ƙwayoyin jini.

14. Kusan rabin karayar da take afkuwa ga manya na faruwa ne a ƙasusuwan damatsa, wato dantsen sama ko na ƙasa.

15. Nauyi, ƙwari da aikin ƙashi na samar da ƙwayoyin jini duk suna ƙaruwa da motsa jiki / atisaye akai-akai, kamar yadda suke raguwa da rashin motsa jiki / atisaye.

#Ƙwarangwal
#HumanSkeleton