Responsive Ads Here

Sunday, August 17, 2025

Medicine (Magani)💊💉

ABUBUWANDA YA KAMATA KU SANI GAMEDA MAGANI:

via Dom-Domty Medicine Store.

 Ka taɓa tambayar kanka a duk lokacin da ka ci karo da masu irin wannan tallar cewa waɗanne irin magunguna suke siyarwa kuma menene dokar su a Nigeria?, ko kayi tunanin haka kawai suke siyar da magunguna yanda suka ga dama ba wanda ya damu da abinda suke yi?.

Tambayoyin suna da yawa amma yana da kyau ka fahimci tsarin tallar su a matakin da suke da kuma irin magungunan da suke siyarwar a babin dokar ƙasa. A yadda gwamnatin Nigeria ta tsara, an tsara magunguna ne a mataki kashi 3 kamar haka:


1) Na farko sune Over the Counters

2) Na Biyu sune Essential Drugs

3) Na uku sune Control Drugs



Ga bayanin su don ku fahimta sosai:


💢Kashi na farko sune muke ƙira da Over the Counters drugs wato OTC: Waɗannan magungunan sune waɗanda koda yaushe akwai su a ko'ina a faɗin duniya - walau a asibiti, chemist, stores har zuwa kan wurin irin waɗannan mutanen da na ɗora hoton sa. Abinda ya sa ake ƙiran su da OTC Drugs shine saboda ana buƙatar su a koyaushe kuma a kowanne irin muhalli sannan koda anyi Overdose ɗin su basu fiya haifar da matsala ba. 


Irin waɗannan magungunan sune kamar su Paracetamol, Vitamin C, Amoxicillin, Flagyl, Sudrex, Antimalarial, Diclofenac, Ibuprofen, Limotil, da iri iren su. Za'a iya baka waɗannan magungunan koda babu katin sheda daga asibiti sakamakon basu da wata illa ta zahiri sannan kuma ana yawan amfani da su on daily basis. 


Wannan ne dalilin da yasa masu tallar magani kamar irin waɗannan suke cin karen su babu babbaka saboda duk inda za'a je a dawo zaka tarar 98% na magungunan da suke siyarwar OTC ne kuma an yarda su siyar da su ɗin. Sai dai duk ranar da NDLEA suka kama su da wata muguwar ƙwaya, gaskiya zaka tausaya musu saboda irin wahalar da suke sha - shiyasa basa garajen yawo da ita, haka kuma basa shakkar tsayawa a bakin titi ko shiga lungu da saƙo saboda sun san inda maganar ta kwana.


💢 Kashi na biyu sune Essential Drugs: Waɗannan sune magungunan da ake samun su a asibiti tare da rubutun likita ko babban ma'aikacin jinya a katin shedar ka na asibiti. Kusan duk magungunan da suke layin OTC ɗin sune dai a Essential Drugs ɗin, sai dai magunguna irin su Ceftriaxone, Ƙarin ruwa, Allurai da kayan wanke ciwo ko ɗaure wani rauni duk suna cikin wannan layin ne. 


Shiyasa indai ka je Chemist ko wani store siyan maganin da suka danganci wannan layin na Essential Drugs, zaka ji sunce ina katin ka? saboda zai yi wahala su ɗauko su baka da garaje ba tare da shedar rubutun kati ba saidai idan sun san kana aiki a asibiti ne musamman idan kasan magunguna. 


💢 Kashi na uku wanda shine na ƙarshe sune muke ƙira da Control Drugs: Abinda yasa ake ce musu Control Drugs shine hatta ma'aikatan asibitin ma ba kowa bane yake da kusanci wajen ganin maganin ma ballantana har ya samu damar ɗauka ko yin amfani da su. Magunguna ne masu haɗarin gaske shiyasa suka zama under strong control. Kai koda ace jinyar ka ta shafi buƙatar ayi amfani da su a kan jinyar ka, kai ɗin ma zai yi matuƙar wahala ka same su haka kawai sai da babban dalilin yin amfani da su ɗin. 


Misalin da zan iya baka kan waɗannan Control Drugs ɗin sune kamar maganin da ake amfani da su wajen yin tiyata, maganin harbin kunama, cizon kare, ko saran maciji. Maganin zubar da ciki, maganin saka bacci mai nauyi ko kwantar da hankali, ko kuma maganin da ake baiwa masu taɓin hankali a psychiatry. Wannan ne dalilin da yasa ba zaka taɓa ganin maganin psychiatry ba a Chemist ɗin garin ku haka kawai da garaje. 


A dunƙule dai wannan shine raben raben da gwamnatin Nigeria ta tsara siya da ajiyar magani a kowanne muhalli. Saboda haka ba kowanne magani bane zaka tsince shi a kasuwa ko a Chemist haka kawai don kana da jinya. 



Wasu lokutan ma ko da kuɗin ka sai da tsananin rabon ka sannan zaka samu. 

- via-the2brothers-links✍️

Saturday, March 8, 2025

Iftar Mubarak

 AYYUKA MUHIMMAI GUDA HUDU DA YA KAMATA AYI YAYIN BUDA BAKI:

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اَللّهِ الرَّحْمنِ الرَّحِيمِِ



Dukkan mai Azumi yana da aiyukan da ya kamata yayi su Kafin yayi Buda Baki, aiyuka ne masu sauki, da kuma Tarin Lada:


Na Farko (1) : 

Kafin mai Azumi ya sanya wani abu a Bakinsa, zai ce:

اللهم لك صمت وعلى رزقك افطرت وعليك توكلت

Duk wanda yayi wannan Addu'a kafin yayi Buda Baki, yana da Ladan dukkanin mutanen da suka yi Azumin wannan Rana.




Na Biyu (2) : 

Yana daga cikin abubuwan da mai Azumi zai yi kafin ya Buda Baki, fadin:

بسم الله الرحمن الرحيم

يا واسع المغفرة اغفرلي

Duk wanda yayi wannan Addu'a yayin Buda Baki, Allah t. zai Gafarta mishi Zunabansa baki Daya.




Na Uku (3) :

 Yana da Muhimmanci ga mai Azumi ya Karanta Suratul Qadri kafin yayi Buda Baki:

انا انزلناه في ليلة القدر

Wanda ya Karanta Suratul Qadri, Lokacin Sahur da Kafin yayi Buda Baki, zai samun Ladan wanda wanda ya samu Shahada ta hanyar Zubar da Jininsa.




Na Hudu (4) : 

Kowani mai Azumi yana da Kyautan Addu'a Karbabbiya yayin Buda Baki, kada ka manta baka yi Addu'a na neman Bukatan Duniya da Lahira ba, a kowani Ranan da kakai Azumi.



Allah ya Karbi Sa'ayinmu na Azumin da sauran Ibadodinmu a wannan Wata mai Alfarma, Albarkacin Ahlul Kisa'i (AS).

Sannan Muna Fatan Zaku Sanya Dom-Domty Medicine Store ( Mai Shagon Da Yaran Shagon, Kai Harma Da Makwabta Gaba Daya) Acikin Addu'o'inku !

Signed: Askary Abdullahi tareda sahalewar P.A Bamatsala.

via-the2brothers-links