Responsive Ads Here

Wednesday, May 31, 2023

 KAMUN LUDAYIN JEMAGE

30-05-2023



....A yau mun garzaya sahar sadar da zumunta ta Facebook domin duba da irin sharhi da al-ummar kasa keyi gameda sauyi na sabon gomnati da akayi, ga kadan daga cikin abinda muka sa mo muku.


Hazbiya ta dafa ƙawarta Kurciya ta ce "Jiya fa an sha shagalin rantsuwa, yau da safe ina farkawa abin da na fara tunawa shi ne, yanzu fa mun bar mulkin Babba-da-jaka mun koma mulkin Jemage, lallai duniya na gudu!"


Kurciya ta yi murmushi sannan ta ce "Dama ai duk girman gona akwai kunyar ƙarshe, yanzu dai Jemage ne ya karɓi ragamar tafiyar da mulkin dajin nan, Allah ya yi jagora"


Kanari da ke gefe ta amsa da "Ameen! Sai dai ni a bayanan da Jemage ya yi jiya, sun yi ma'ana amma maganar gaskiya tallafin nan da ya ce zai cire ya tsaya mun a rai!"


Hazbiya ta ce "Ni ma haka, amma ya ce don a samu isassun kuɗaɗe ne don ai aiwatar da ayyuka masu muhimmanci ne, sannan kuɗin tallafin ma an ce su shirwa ne ke cinyewa da daɗewa"


Tattabara wadda tunda aka fara zance ba ta ce kanzil ba, ta ƙuta ta ce "Ni tsoro na, kar su shirwa su zagaye su cinye kuɗaɗe ayyukan, kun ga kenan an yi biyu babu, ba tallafi babu ayyuka, Allah ya tsare!"


"Ƙwarai kuwa, sannan na ji Jemage ya naɗa muƙamai har uku, amma duk ƴan'uwansa ya naɗa, an ce babu tsuntsu ko ɗaya, kar fa Jemage ya yi koyi da  Babba-da-jaka?" Kurciya ta faɗa cikin sassanyar murya.


Gado ya ɗaga murya ya ce "Allah dai kar ya maimaita mana mulki irin na Babba-Da-Jaka, an sha gwagwarmaya fa jama'a, mu dai taya Jemage da addu'a, Allah ya ba shi ikon sauke nauyi"


"Ameen!" Tsuntsaye su ka amsa.



An hango Babba-da-Jaka na ba da umarni da a ƙaro na'urar sanyaya sheƙa, a tsohuwar sheqarsa !

Duniya Kenan.

              ☆via-the2brothers-links☆