
Abubuwan Ban Mamaki 15 Gameda Kwarangwal: Kwarangwal shine jerin kasusuwan jiki kuma ginshikin dake rataye da dukkan sassan jiki.1. Akwai ƙasusuwa daban-daban har guda 206 a jikin mutum. 2. Jarirai sun fi manya yawan ƙasusuwa, a yayin da manya ke da ƙasusuwa guda 206, jarirai na da ƙasusuwa kusan 270, inda yawansu zai ɗinga raguwa yayin girmansu saboda haɗewar wasu daga cikin ƙasusuwan har su zama dai-dai da na manya.3. Fiye da rabin...