Kwarangwal shine jerin kasusuwan jiki kuma ginshikin dake rataye da dukkan sassan jiki.
1. Akwai ƙasusuwa daban-daban har guda 206 a jikin mutum.
2. Jarirai sun fi manya yawan ƙasusuwa, a yayin da manya ke da ƙasusuwa guda 206, jarirai na da ƙasusuwa kusan 270, inda yawansu zai ɗinga raguwa yayin girmansu saboda haɗewar wasu daga cikin ƙasusuwan har su zama dai-dai da na manya.
3. Fiye da rabin ƙasusuwan ƙwarangwal — ƙasusuwa 106, suna nan a tattare a hannaye, tsintsiyoyin hannu, da kuma tafukan sawu.
4. A tafin sawu ɗaya kawai, akwai ƙasusuwar har guda 26.
5. Hannu haɗi da tsintsiyar hannu na ɗauke da ƙasusuwa har guda 27.
6. Ƙashin cinya shi ne ƙashi mafi tsayi kuma mafi ƙwari a jikin mutum.
7. Ƙashi mafi ƙanƙanta kuma mafi ƙarancin nauyi shi ne ƙashin 'stapes' da ke tsakiyar cikin kunne, ɗaya ne daga cikin ƙasusuwa uku da ke tsakiyar cikin kunne da ke temaka wa wajen sarrafa sauti.
8. Ƙasusuwa na gama tsayin ne bayan balaga zuwa wajejen shekara 25, amma kauri, nauyi da ƙwarin ƙashi za su ci gaba da caccanzawa tsawon rayuwa.
9. Ƙashin 'hyoid' shi ne ƙashi ɗaya tak da bai jingina da wani ƙashi ba. Wannan ƙashi mai sifar "V" na nan tsakanin maƙogaro da tushen harshe.
10. Muhimman sinadaran ginin ƙashi sun haɗa da kalsiyam (calcium), fasfaras (phosphorus), sodiyam (sodium) da sauransu. Don haka cin abincin da ke ɗauke da waɗannan sinadarai na temakawa wajen gina ƙashi.
11. Kamar yadda ƙwarangwal ya zama ginshikin jiki, haka nan tsokokin jiki sune ke samar da ƙarfi / yunƙurin da ke motsa sassa ko gaɓɓan jiki.
12. Ƙwarangwal na samar da kariya ga muhimman sassan jiki kamar ƙwaƙwalwa da ke ƙunshe cikin ƙoƙon kai, laka da ke ƙunshe cikin kwaroron ƙashin gadon baya, ƙwayar ido da ke cikin gurbin ido da kuma zuciya da huhu da ke cikin kejin haƙarƙari.
13. Dogayen ƙasusuwan ƙwarangwal da ke ƙunshe da ɓargo a cikinsu na daga cikin sassan jiki da ke samar da ƙwayoyin jini.
14. Kusan rabin karayar da take afkuwa ga manya na faruwa ne a ƙasusuwan damatsa, wato dantsen sama ko na ƙasa.
15. Nauyi, ƙwari da aikin ƙashi na samar da ƙwayoyin jini duk suna ƙaruwa da motsa jiki / atisaye akai-akai, kamar yadda suke raguwa da rashin motsa jiki / atisaye.
#Ƙwarangwal
#HumanSkeleton