Responsive Ads Here

Thursday, February 13, 2020

Happy Weekend (2)

My Letter To Corona Virus:



Dear CORONA VIRUS,
I want to beg you in the name of the poor in Nigeria, please don't listen to the empty boasts of our Nigeria leaders. Our leaders don't know what the are saying. How can they say they are ready and prepared for you?

Abeg Sir, na lie, na slip of tongue. Just yesterday they said they have voted N680m to prepare for you, just imagine!! How much is that?

Sir, Look at how your Younger brother, Lassa Fever, is dealing with our people, your brother is already in 28 states of Nigeria unstoppable talk less of you.

Dear CORONA VIRUS, your birth place, China, with all her sophistications couldn't withstand your anger.
*China is overwhelmed,
*WHO is overwhelmed,
*Advanced countries are scared,
*Nigeria is boasting.
(Snails do not attend a meeting of Animals with horns).

Please in our poor country sake, don't come here, we can't handle you, we don't have the money, we don't have any hospital, no Power, we don't even have hand gloves and nose masks, our Doctors are afraid of you.
Our Government is joke.

Thank you sir






Signed:
thë2ßrøthêrs

Thursday, February 6, 2020

Kunne/Ear

CIWON KUNNE   



Ita kunne kanta an kasa shi bari uku (3) :
1- Outer ear -  wajen kunne .
2- Middle ear - Tsakiyar kunne
3- Inna ear - Cikin kunne .

Mafi yawan ciwon kunne da mutane suke complaining ciwon tsakiyar kunne ne (Otitis media) .


ME YAKE KAWO CIWON TSAKIYAR KUNNE :  

Yana daga cikin abubuwanda suke kawo ciwon tsakiyar kunne :
1- kwayar cututtuka kamar su :   
a- Bakteria   
b- Virus
 Amma mafi yawa bakteriya ne, wadannan kwayoyin cututtukan yawanci suna samun hanyar shiga ne ta makogoro zuwa tsakiyar kunne. ( akoi hanyar da tahadasu dama).

2- Anasamun ciwon kunne ta dalilin shigan wani Abu kamar Burbushin Kura, Gashin magye da sauransu ( Allergies).


HALAMUN CIWON TSAKIYAR KUNNE :  

1- Mutun zaiji kamar wani abu ya cika masa kunne .
2- Rashin ji sosai
3- Zubar da ruwa a kunne
4- Jin zafi a cikin kunne .
5- kaikayin
6- Zazzabi da ciwon kai .


MENENE ALAKAR MURA DA CIWON KUNNE :  

Gaskiya akoi alaka tsakanin mura da ciwon kunne, mafi yawan mura yana kama hanci da makogoro kuma idan Baku manta ba munce akoi hanyar da tahada tsakanin Makogoro da Hanci dakuma tsakiyar kunne.  Kamar yadda mukace kwayoyin cutar bakteriya, da virus da kuma burbushin kura su suke kawo ciwon kunne. To wadannan kwayoyin cutar su suke kawo Mura kuma suna samun hanyar shiga kunne ta wannan hanyar da tahada tsakanin makoro, hanci da kunne.


SHIN DIGAWA KUNNEN MAN ZAITUN YANA MAGANI CIWON KUNNE :  

Kuskure ne digawa kunne man zaitun, bama man zaitun ba ko maganin ciwon kunne irin su gentamycin bai kamata a digawa kunne ba, in bada izinin likita ba.  Dalili shine wani lokocin ana samun fujewan dodon kunne (rupture of earwax) lokocin da ake ciwon kunne to ko wanne  irin abu idan yawuce can ciki zai iya kawo matsala.


MAGANIN CIWON KUNNE :  

Tabbas duk wani ciwon kunne da kwayoyin cutar bakteriya takawosu ana amfanida ANTIBIOTICS wajen treatment , hakanan wanda aka samu da dalilin Burbushin kura ana amfani da ANTIHISTAMINES.



ABUN LURA DA HANYOYIN KARIYA:

1- Kada a wanke kunnen yaro wai dan sabida yana ruwa. Bincike ya nuna akoi sinadarai guda goma a tsakiyar kunne wanda aikinsu shine hana shigar kwayoyin cuta, tham a garin wanke dauda idan aka wane wadannan sinadaran shikenan anbudewa kwayar cuta kofa.

1- Gangar tsakiyar kunne musamman na yara batada kwari a garin wankewa zai iya fashewa wanda hakan zai iya kawo rashin ji kwatakwata.

2- Shayar da yara da nonon uwa zalla ba tareda an garwaye shi da ruwa ko Abinci.  Kuma kada abawa yaro nono a kwance sabida yakan iya kawo ciwon kunne.

3- Kada ayi amfani da tsinke ko fiffigen tsunstu wajen tsosawa yaro kunne ko babba domin tana kawo rauni ga gangan tsakiyar kunne.

4- kada a jiye yaro kusada inda hayakin taban sigari yana tashi domin shima yakan taimaka wajen kawo wannan matsalar. 

5- Yiwa yaro allurar rigakafi da yana rage wannan matsalar, musamman allurar rigakafi irinsu na kyeda da Kuma na mura Mai kama hanyar numfashi.

6- Ba'a digawa yaro maganin ciwon kunne a kunne ko wacce eri saida amincewar likita. 






Lafiya Uwar Jiki, Babu Mai Fushi Dake!

....Lalle wannan magana haka take, domin a 'yan kwanakin nan an binciki file dina (nayi rashin lafiya) Wanda hakan yasani na qara fahimtar ba arzikin da yakai na lafiya a duk  fadin duniyar nan. Wato ciwon nan daya rafkeni.....(abin sai dai shukran).
Hakan nema yasani yin wannan rubutun domin na tunatar abisa ga dogaro da wannan ayar: “And Keep Reminding because reminding Benefits the believers." (5:155)

Ya Kai dan-uwa a duk sa'dda da Allah (s) ya wayi gari ka tashi ka jika lafiyarka qalau to 
Ka good masa bisa ga wannan babbar baiwa da ni'ima da yayi maka!

Da haka nake cewa, Allah ka qara mana lafiya da Arziqi mai albarka. Marasa lafiya da suke a gida da asbiti suma ubangiji Allah ka sauwaqe musu!


Uhm! A wancan lokacin da nake kwance, abincima ina son naci amma bazai ciwuba sakamakon bakina ya Zama testless. Ko tuwo aka kawo inaji ina kallo Saidai.....

 Amma Yanzu Alhamdulillah! Lafiya ta samu, ga masu niyyar kawo mini lemo da kaza to kofa a bude take! Hahhhh!

Eh Baza mu manta da irin dawainiyar da su Sufi suka Shiga ba, Allah ya saka da alheri!

Signed:
thë2ßrøthêrs

'Yar Wuya/Beli

CIRE YAR WUYA DA KUMA BELI A JARIRAI. 

....Abisa duba ga wasu daga cikin al'adunmu na Hausawa, Hakan yasani wasu 'yan nazarce- nazarce wanda har a qarshe ya kaini ga yin rubutu Akan maudu'in dake a sama, tare kuma da Kokarin samo amsoshin wasu tambayoyi da nayi kamar haha:

 Shin hakan yana da wani fa’ida a likitance? Duba da irin yanda yaran ke shan wahala bayan cire mu su. Me yasa ake cirewa? Sannan me zai faru idan ba’a cire ba?! 

A mahanga ta likitanci cire wadannan abubuwan ba shi da wani fa’ida (medical benefit), sai dai ma ayi batun illa. Sannan duk dalilan da aka kawo na cirewar (ga masu cirewa kenan) idan mutum ya yi nazari, zai ga cewa ba su bayar da wata ma’ana ba.

A addinance kam akwai ‘controversies’ da yawa akan abun. Wasu Malaman sun tafi akan cewa wajibi ne a cire, wasu kuma sun ce yana da kyau a cire (amma ba wajibi ba), wasu kuma sun dauki matsayar cewa kar a cire.


A zahiri dai, ya fi kama da al’ada kawai, wacce ta fi shahara a kasar Hausa. Kuma kamar yanda muka sani, akwai al’adu da yawa wadanda suke cutarwa (Harmful Traditional Practice) ga lafiyar mutum, amma ana yin su. Cire ‘yar wuya da kuma beli sun fado cikin misalan wadannan al’adun; wankan jego da tafasasshen ruwa, shan kunun kanwa wanda ya wuce qa’ida ga mata masu juna biyu/ masu shayarwa, yin shayi/kaciya ga mata, dss; na kadan daga cikin wadannan al’adun.



- MENENE BELI? 

Shi ‘Beli’ sunan shi “Uvula” a likitance. Shi ne ya rufe tsakanin baki da makogoro.. (Da yake likitanci ba da Hausa ake koyar da shi ba, wasu lokutan sunayen kan iya canjawa ‘depending’ on yankin da mutum ya ke).

Babu wani ‘Medical benefit’ na cire shi a jikin jariri gaskiya. Wadanda suke cirewa sun yi ‘theorizing’ cewa yana hana gudawa da amai (amma ba su yi bayanin ya hakan ke faruwa ba), yana kawo shakewa idan ana shayar da jariri, sannan kuma wai saboda tsoron kar ya kumbura idan cuta ta kama shi.

Amma kuma illar cire shi ya fi yawa. Kama daga ballewar jini, da kuma kassara ‘normal anatomical presentation’ na bakin mutum, yiwuwar wucewar abu daga bakin mutum zuwa cikin hancin shi, da kuma daga baki zuwa huhu idan jariri, dss.

Babu wani dalili da zai sanya a cire ma jariri Beli matukar ba wai yanayi ya bada hakan ba ne, kamar misali kamuwa da wata cuta, dss.




- MENENE 'YAR WUYA? 

Kamar yanda nace Hausa na bambanta. Wasu na kiran shi hakin wuya, wasu kuma ‘yar uwa. Kila a wani wajen ana kiran shi wani abu ne ma daban.

Shi kuma ‘yar wuya shi ne “Palatine tonsil” [wannan shi aka fi cirewa, kuma shi ya fi hadari]. Saboda ko ba komai su “tonsils” generally kamar misalin barikin sojoji ne a kasa, inda ya ke tattara sojoji ya basu horo. A cikin ‘tonsils’ ne ake samun ‘immune cells’ [wadanda kamar su ne sojojin jikin mutum da ke yaqi da cututtuka] da ke kare jiki daga kamuwa da wasu kwayoyin cututtuka. Ka ga idan aka cire shi (tonsil) daga jikin mutum, zai zama kamar an cire sojoji daga kasa ne a lokacin yaqi ko?

Duk wata kwayar cuta da ta shiga bakin mutum kafin ta je makogoro, sai wadannan “Palatine tonsils” din [su ne kuma ake ce ma ‘yar uwa] sun tare ta, sun yaqe ta domin su hana ta wucewa. Idan babu kai tsaye zata wuce zuwa makogoro kenan; daga nan kuma sai inda Allah Ya yi. Akwai shi kan shi makogoro, akwai ciki, akwai hanji, akwai hanta, akwai huhu; duk cuta zata iya zuwa musu daga baki.

Binciken likitoci ya tabbatar da cewa, jariran da ake cire ma ‘yar wuya din nan sun fi kamuwa da cututtuka fiye da wadanda ba’a cire musu ba. Musamman cututtukan da suka danganci baki, hanci da kuma makogoro.

Akwai yanayin da zai iya bayar da cewa a cire din, misali idan suka kamu da cuta suka kumbura da kuma barazanar yada cutar zuwa wani sashe daban na jikin mutum. Ana cirewa, ba su kadai ba ma; har sauran “tonsils” ana iya cirewa idan yanayin cuta ya bada. Amma idan babu wani dalili, sam bai kamata ake cirewa jarirai ba.




A takaice dai ba shi da wani fa’ida a likitance cire wadannan abubuwan. Kowanne daga cikin su yana da amfani a jikin jariri. Jikin dan Adam shi ne cikamakon halitta, duk abun da ka ga Allah (T) Ya halitta a jikin dan Adam, akwai amfanin shi. 

Allahu a’alam..


          >>>>> Yours Dom-Domty <<<<<


....Ku Kasance da shafin Dom-Domty a Koda yaushe, domin samun bayanai da fadakarwa da suka shafi harkar kiwon lafiya!




   Sannan Angaida Yara Manyan Gobe!




Signed:
thë2ßrøthêrs